Vous-êtes ici: AccueilCulture2021 05 03Article 450572

BBC Hausa of Monday, 3 May 2021

Source: BBC

'Ba wata yarjejeniya da aka cimma da Iran kan musayar fursunoni'

Nazanin Zaghari-Ratcliffe Nazanin Zaghari-Ratcliffe

Jami'an gwamnatin Birtaniya da takwarorinsu na Amurka sun musanta wani rahoto daga Iran da ke cewa, kasashen uku sun cimma wata yarjejeniya ta musayar fursunoni.

An danganta rahoton ne daga wani labari da gidan talabijin na gwamnatin Iran ya yi.

Rahoton wanda ya fito daga Tehran babban birnin Iran na nuna cewa an cimma matsaya tsakanin kasashen uku Amurka da Birtaniya a bangare daya da ita kuma Iran a daya bangaren kan sakin wasu Amurkawa hudu da aka daure a Iran din.

Kan hakan ita ma Amurka za ta saka da sakin wasu iraniyawa hudu da ta daure, sannan kuma za ta saki kadarorin Iran din na dala miliyan dubu bakwai da ta dakatar.

Sai dai Amurkar ta musanta wannan labari, inda shugaban ma'aikata a fadar gwamnatin kasar Ron Klain a wata hira da tashar talabijin ta CBS da Amurkar ya ce labarin karya ne kawai.

Ya ce: ''Ina tababatar ma cewa abin takaici wannnan rahoto ba gaskiya ba ne. Babu wata yarjejeniya ta sakin wadannan Amurkawa hudu. Muna kokari matuka gaya domin ganin an sake su.

A ko da yaushe muna tayar da wannan magana da Iran da kuma masu shiga tsakaninmu. Amma dai zuwa yanzu babu wata yarjejeniya ta maido da wadannan Amurkawa hudu gida.'' In ji shi.

Haka kuma rahoton na Iran ya ce, gwamnatin kasar za ta saki wata 'yar Birtaniya 'yar asalin Iran din Nazanin Zaghari-Ratcliffe, idan Birtaniya ta biya Iran wani tarin bashi da Iran din ke binta.

Dangane da wannan batun shi kuma, ma'aikatar harkokin wajen Birtaniya a Landan ta ce, tana nan dai tana duba wasu hanyoyin daban dangane da bashin.

Mijin matar, Richard Radcliffe, ya yi maraba da wannan rahoto daga Tehran a matsayin wata alama mai kyau ko da yake ya ce babu wani bayani da aka yi musu kan wannan takaddama da ta dae ana ta yi.

A makon da ya gabata bangaren shari'a na Iran ya sanar da cewa an kara wa Nazanin hukuncin karinshekara daya a gidan yari saboda yada farfagandar karya a kan kasar Iran.

Shi dai gidan talabijin na Iran na karkashin ikon masu ra'ayin mazan-jiya ne wadanda ba sa goyon bayan tattaunawar da ba ta gaba da gaba ba tsakanin Iran da Amurka wadda ake shirin yi a Vienna.

Tattaunawar na da nufin mayar da Iran da Amurka kan teburin yarjejeniyar nukiliya ta 2015 da kuma dage wa Iran takunkumin da Amurka ta sanya mata.

Ranar Juma'a ne za a yi zagay na gaba na tattaunawar, inda dukkanin bangarorin ke sa ran cimma yarjejeniya nan da mako uku.

Kila a kai ga cimma matsaya da za ta kai ga Amurka ta saki kadarorin Iran din na biliyoyin dala da ta rike a waje.

Sai dai masu tsattsauran ra'ayin rikau a Iran din na zargin masu shiga tsakani na bangaren kasar a Vienna da bayar da kai bori ya hau ga bukatun Amurka na abin da suka nuna rainin hankali.

A ranar 18 ga watan Yuni za a yi zaben shugaban kasa a domin maye gurbin Hassan Rouhani da ya yi wa'adi biyu. Kafin zaben ana ganin yanayin siyasar kasar zai zafafa inda masu ra'ayin rikau za su so su yi duk abin da za su iya domin su karbi mulki, wanda wannan ne abin da ya rage wa masu hamayya da su.