BBC Hausa of Monday, 17 May 2021
Source: BBC
A ranar Lahadi ne Ƙungiyar ƙwadago a Najeriya NLC ta kira yajin aiki a jihar Kaduna inda al'ummar jihar suka tsinci kansu cikin duhu - babu wutar lantarki saboda matakin.
Mahukuntan hukumar samar da hasken wutar lantarki a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya sun bi sahun yajin aikin inda suka nemi gwamnati da ta janye matakin da ta ɗauka na korar sama da ma'aikata 7,000.
Shugaban Ƙungiyar NLC a jihar, Kwamared Ayuba Magaji Sulaiman ya ce matakin da za su ɗauka shi ne durƙusar da harkoki a jihar daga ranar Lahadi har tsawon kwana biyar.
Rahotanni na cewa gwamnatin Nasir El Rufa'a ta ɗauki matakin rage yawan ma'aikatan jihar.
Gwamnatin ta ce ta ɗauki matakin ne saboda yawan kuɗaɗen da take kashewa duk wata wajen biyan albashi.
Amma shugabancin NLC a jihar ya yi fatali da matakin.
"Kawai gwamnati ta yanke hukuncin korar sama da ma'aikata 7,000 ba tare da sanarwa ba ko kuɗaɗen sallama," in ji Shugaban NLC.
"Mutane ne da iyalinsu suna da mutanen da suka dogara a kansu, don haka wannan matakin ba dai-dai ba ne.
"Wannan ne ya sa muka shiga yajin aiki sannan sauran kungiyoyin ƙwadago sun shirya don shiga yajin aikin har sai gwmanati ta soke matakin korar ma'aikatan."
Ƙungiyoyin ƙwadago ƙarƙashin NLC sun tura takarda ga ƙungiyoyin ma'aikata domin su shiga yajin aikin.
Yadda yajin aikin zai shafi jama'a
Kamfanin samar da wutar lantarki a Kaduna ya fitar da sanarwa inda ya sanar da abokanan hulɗarsa cewa za su fuskanci katsewar wutar lantarki saboda yajin aikin.
"Kamfanin rarraba hasken wutar lantarki ya amsa kiran NLC inda ya katse cibiyoyin ba da wutar lantarki mai karfin 33KV."
NLC ta kuma yi kira ga masu sana'ar babur da babur mai kafa uku su shiga yajin aikin.
Cikin takardar, kamfanin samar da wutar lantarki a Kaduna ya bukaci wadannan kungiyoyin su shiga yajin aikin: