Vous-êtes ici: AccueilCulture2021 03 15Article 449654

BBC Hausa of Lundi, 15 Mars 2021

Source: BBC

Jami'an tsaro sun murƙushe yunƙurin sace ɗaliban sakandare 307 a Kaduna

Daliban ne suka sanar da jami'an tsaro lokacin da ƴan bindigar suka shigo makarantar Daliban ne suka sanar da jami'an tsaro lokacin da ƴan bindigar suka shigo makarantar

Gwamnatin Kaduna ta ce ƴan bindiga sun sake kai hari wata makarantar sakandaren Ikara inda suka yi yunƙurin sace ɗaliban makarantar.

Kwamishinan tsaro da lamurran cikin gida na jihar Kaduna SAmuel Aruwan wanda ya tabbatar da harin ya ce ƴan bindigar sun abka makarantar sakandaren Kimiya GSSS Ikara ne da tsakar daren Asabar zuwa wayewar safiyar Lahadi.

Ya ce daliban ne suka sanar da jami'an tsaro lokacin da ƴan bindigar suka shigo makarantar.

"Nan take jami'an tsaron da suka hada da sojoji da ƴan sanda da ƴan sa-kai suka ruga makarantar tare da yin artabu da yan bindigar, suka kore su," in ji shi.

Ya ce,"an ceto dalibai 307 ba tare da sun samu wani rauni ba" a harin da sojoji da suka murƙushe.