Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 05Article 450622

BBC Hausa of Wednesday, 5 May 2021

Source: BBC

'Yan Real Madrid da za su kara da Chelsea a Ingila

Real Madrid ta lashe Champions League karo 13, Chelsea sau daya Real Madrid ta lashe Champions League karo 13, Chelsea sau daya

Real Madrid ta je Stamford Bridge domin buga wasa na biyu na daf da karshe a Champions League da za su fafata ranar Laraba.

A makon jiya ranar Talata kungiyoyin suka tashi 1-1 a Spaniya a wasan farko na daf da karshe a gasar ta Zakarun Turai.

Tuni kocin Real Madrid, Zinedine Zidane ya bayyana 'yan wasan da za su fuskanci Chelsea a wasa na biyu a Stamford Bridge.

Duk wadda ta yi nasara za ta buga wasa ne da Manchester City wadda ta kai karawar karshe a karon farko a Champions League, bayan da ta doke PSG da ci 4-1 gida da waje.

'Yan wasan Real Madrid da suka je Ingila:

Masu tsaron raga:

Courtois da Lunin da kuma Altube.

Masu tsaron baya:

E. Militao da Sergio Ramos da Nacho da Marcelo da Odriozola da Mendy da kuma Miguel.

Masu buga tsakiya:

Kroos, Modric da Casemiro da Isco da Valverde da Arribas da kuma Blanco.

Masu cin kwallaye:

Hazard da Benzema da Asensio da Vini Jr. da Mariano da kuma Rodrygo.