Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 05Article 450622

BBC Hausa of Wednesday, 5 May 2021

Source: BBC

'Yan Real Madrid da za su kara da Chelsea a Ingila

Real Madrid ta je Stamford Bridge domin buga wasa na biyu na daf da karshe a Champions League da za su fafata ranar Laraba.

A makon jiya ranar Talata kungiyoyin suka tashi 1-1 a Spaniya a wasan farko na daf da karshe a gasar ta Zakarun Turai.

Tuni kocin Real Madrid, Zinedine Zidane ya bayyana 'yan wasan da za su fuskanci Chelsea a wasa na biyu a Stamford Bridge.

Duk wadda ta yi nasara za ta buga wasa ne da Manchester City wadda ta kai karawar karshe a karon farko a Champions League, bayan da ta doke PSG da ci 4-1 gida da waje.

'Yan wasan Real Madrid da suka je Ingila:

Masu tsaron raga:

Courtois da Lunin da kuma Altube.

Masu tsaron baya:

E. Militao da Sergio Ramos da Nacho da Marcelo da Odriozola da Mendy da kuma Miguel.

Masu buga tsakiya:

Kroos, Modric da Casemiro da Isco da Valverde da Arribas da kuma Blanco.

Masu cin kwallaye:

Hazard da Benzema da Asensio da Vini Jr. da Mariano da kuma Rodrygo.