BBC Hausa of Tuesday, 9 March 2021
Source: BBC
A Najeriya, yayin da ake ci gaba da rubibin yin rijistar lambar dan kasa wato NIN wadda hukumomi suka wajabta wa 'yan kasar, ga alama an bar al'umar karamar hukumar Kanam da ke jihar Filato a baya nesa ba kusa ba - saboda babu cibiyar yin rijistar ko daya a fadin yankin.
Don haka ne galibin jama'ar yankin ba su yi rijistar ba, yayin da wadanda ke kokarin yi kuma sai sun tafi wasu kananan hukumomi ko ma wasu jihohin kafin su samu damar yin rijistar.
Jama'ar karamar hukumar Kanam, wadda ke daya daga cikin kananan hukumomi mafiya girma a jihar Filato, ta fuskar fadin kasa da yawan jama'a, suna kukan cewa an mai da su saniyar ware, tamkar ba a Najeriya suke ba.
Suna wannan kuka ne sakamakon tsame su daga tsarin rijistar shaidar dan kasa da ake yi a fadin kasar -inda babu cibiyar yin rijistar ko daya a duk fadin yankin duk da muhimmancin rijistar wajen yin huldodi da suka jiɓinci hukuma.
Wannan lamari ya jefa jama'ar yankin cikin matukar kunci, da bacin rai da kuma zullumi.
'Muna shan wahala ana mana gori'
Rashin yin rijistar ga jama'ar Kanam ya zama tamkar ruwan dare saboda rashin samun damar yin hakan. Su kuwa 'yan kalilan da ke ƙuƙutawa su tafi wasu yankunan domin yin rijistar, suna bayyana irin bakar wahala da suke fuskanta.
A cewarsu, sukan bar ayyuka da sana'o'insu na neman abinci, su yi tafiya mai nisa, su kashe kudin mota, sannan duk karamar hukumar da suka tafi domin yin rijistar sukan sha gori da habaici.
Haka nan ga matukar cunkoso da ya saba ƙa'idar kauce wa cutar korona.
Wani mazaunin karamar hukumar ta Kanam, Abdullahi Suleiman Suwalo, ya ce shi a karamar hukumar Kanke ya yi rijistar, sannan daga bisani ya ɗebi iyalansa zuwa karamar hukumar Wase domin su yi tasu.
Ya kuma ce a wasu wuraren da suke zuwa har ana yi masu gori, da kuma zargin cewa suna toshe wa wasu mazauna yankunan guraban rijista.
Abdullahi ya ce da kyar suke samun yin rijistar domin ''yawancin mutane ma kwana suke yi a wurin, kai wasu ma sai sun yi kwana uku, kwana hudu.''
Ya kara da cewa cunkoson jama'a kuwa kamar ana cin kasuwa kuma ''gaskiya wannan abun ya yi matukar daga mun hankali… kai ba iya ni ba, mutanenmu gaba daya ba sa farin ciki da wannan abu.''
Ita ma wata daliba, Nafisat Abdul, ta ce sai da ta yi tafiya mai nisa zuwa karamar hukumar Wase, inda ta kashe kudi kimanin N2,800 a zirgar-zirgar sufiri cikin yini biyu domin ta samu rijistar.
Nafisat ta ce "gaskiya akwai wahala sosai, sai da na je na dawo. Na yi kwana biyu," tana mai cewa wasu ma ba su da sukunin yin irin wahalar da ta yi wajen samun rijistar ta lambar dan kasa.
Ko da yake galibin jama'ar yankin na Kanam ba su samu damar yin rijistar ba, wasu daga cikin wadanda suka ƙoƙarta suka yi, sun shaida wa BBC cewa sun dage suka yi rijistar ne saboda muhimmancinta a matsayinsu na 'yan Najeriya domin kada su rasa alfanun da ke tattare da samun lambar.
"Gwamnatoci ba su yi mana adalci ba"
Karamar hukumar Kanam mai hedikwata a garin Dengi, ita ce kadai karamar hukuma a jihar Filato wadda ba a taba samar mata da cibiyar rijistar shaidar dan kasa ba, amma babu tabbaci ko ita ce daya tilo cikin kananan hukumomi 774 da ke fadin Najeriya.
Yanki ne mai ɗumbin garuruwa da yankunan karkara masu munin hanyoyin mota wadda ta wasu ɓangarorin ta kasance kan iyakar jihar Filato da ke arewa ta tsakiyar Najeriya, da kuma jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin kasar.
Galibin jama'ar yankin manoma ne da makiyaya da kuma 'yan kasuwa.
Mai martaba Sarkin Kanam, daya daga cikin manyan sarakunan gargajiya na jihar Filato, Alhaji Muhammadu Babangida Mu'azu III, ya shaida wa BBC cewa duk da kokarin da suka yi ta yi na tuntubar jami'ai domin ganin an samar da cibiyoyin rijistar a yankin, abin ya faskara.
Ya ce ana ta yi masu alkawarin da ba a cikawa kuma sun kasa fahimtar takamaimai dalilin da ya sa aka maida su saniyar ware.
Sarkin ya ce samun "cibiyar rijistar lambar dan kasa kawai ya zama da wahala? Abin mamaki ne gaskiya. Ko da a cikin hedikwatar karamar hukuma ma babu balle kuma a sauran gundumomi."
Alhaji Babangida ya kara da cewa rashin adalci ne ga talakawan Kanam a ce babu wurin yin rijistar duk da cewa al'ummar yankin suna bayar da gudummowa, da goyon baya da kuma yin biyayya ga gwamnatoci a dukkan matakai tun daga matakin karamar hukuma zuwa jiha da kuma tarayya.
"Mu ma mun cancanci mu samu wannan cibiyar rajista," in ji shi.
Ya kuma ce ko a cikin hedikwatar karamar hukumar ne kawai aka samar da cibiya, to da jama'a za su dan samu sauki, su rika zuwa daga kauyukansu domin yin rijistar, "to amma babu shi gaba daya. Abin damuwa ne a kan jama'armu".
Sarkin ya kara rokon hukumomi da abin ya shafa da su kara kaimi wajen samar wa talakawan yankinsa wuraren yin rijistar.
BBC ta yi kokarin jin ta bakin Hukumar Kula da Shaidar dan Kasa ta Najeriya wato NIMC a jihar Filato da kuma a hedikwatarta da ke Abuja kan matsalar rashin wuraren yin rijistar a yankin, amma kokarin ya ci tura.
To sai dai kuma wata majiya a hukumar wadda ta bukaci a sakaya sunanta ta bayyana wa BBC cewa rashin samar da wuraren rijistar a karamar hukumar Kanam ba zai rasa nasaba da karancin kayan aiki ba.
To amma wasu daga cikin jama'ar yankin na cewa wannan ba gamsasshiyar hujja ba ce a gare su, suna bayyana cewa tsabagen rashin adalci ne hukumomi suka yi masu.
Hakazalika wasu rahotanni na cewa a cikin 'yan kwanakin nan, an samu tsaikon gudanar da aikin rajistar a wasu daga cikin yankunan kananan hukumomin jihar ta Filato wadanda ke da cibiyoyin rajistar. Dalili kuma shi ne na'u'rorin aikin na yawan lalacewa, lamarin da ke kawo cikas ga aikin da kuma kara jefa jama'a cikin kunci da bacin rai.
Mazaunin Kanam Abdullahi Suleiman ya ce kamata ya yi hukumomi su tausaya wa talaka wajen samar da cibiyar rijistar don ''saukaka wa mutane.''
Fargabar toshe layukan wayoyin salula
An fara aikin rijistar lambar dan kasar fiye da shekaru 10 da suka wuce a cibiyoyi daban-daban da nufin samar da bayanan 'yan kasar a wani rumbu guda daya tilo domin taimaka wa wajen tsare-tsaren ci gaban kasar da tabbatar da tsaro.
To amma ba a samu wani ci gaban a zo a gani ba a adadin wadanda suka yi rijistar.
Sai a baya-bayan nan hukumomin Najeriya suka yi shelar cewa za a toshe layukan salula na wadanda ba su da lambar shaidar dan kasa, lamarin da ya sanya 'yan kasar da ba su yi rijista ba cikin fargaba.
Wasu na ta ruguguwar zuwa wuraren rijista, kuma hukumomi sun ce sakamakon wannan umarni da suka bayar, an samu matukar karuwar miliyoyin mutane da suka yi rijista.
To sai dai wani mazaunin karamar hukumar Kanam wanda bai yi rijistar ba, Malam Muktari Muhammad, ya ce ''ni ba zan je wata karamar hukuma in yi rijistar ba domin ba ni da halin barin kauyenmu zuwa wata karamar hukuma, ba ni da kudin mota, abinci ma da kyar mu ke samu, ni da iyali''.
Ya ce ko da yake yana fargabar za a katse masa layinsa na wayar salula, to amma yana fatan gwamnati za ta samar masu da wurin yin rijistar a kusa.
A farkon watan Janairu Hukumar Kula da Sahidar dan Kasa ta Najeriya NIMC, ta shaida wa BBC cewa daga lokacin zuwa makwanni biyu ma'aikatan rijista za su fara shiga unguwa-unguwa a fadin kasar domin yi wa jama'a rijistar.
To amma halin da ake ciki a yanzu ya yi hannun riga da wancan alkawari da hukumar ta yi fiye da watanni biyu da suka gabata.
A bangare guda kuma yayin da karin wa'adin da hukumomi su ka bai wa 'yan Najeriya na su sada lambobinsu na salula da lambobinsu na shaidar dan kasa ko kuwa a tsohe layukan nasu ya zuwa ranar shida ga watan Afirilu, ke karatowa.
Ga alama kiyayewa da wannan wa'adi zai yi matukar wahala ga dimbin mutane kamar al'ummar karamar hukumar Kanam ta jihar Filato inda kawo yanzu babu cibiyar yin rijistar ko daya.
Muddin kuma ba a samu sauyin lamura ba, to akwai yiwuwar dubban masu amfani da wayoyin salula a karamar hukumar - wata kila da ma wasu yankunan Najeriya - su wayi gari su ga an toshe hanyoyin nasu na sadarwar salula - bisa abinda suka yi imanin ba laifinsu ne ba.