BBC Hausa of Tuesday, 9 March 2021

Source: BBC

Neymar ba zai buga wa PSG karawa da Barcelona ba

Neymar ya yi rauni a watan Fabrairu Neymar ya yi rauni a watan Fabrairu

Dan kwallon Brazil, Neymar ba zai buga wa Paris St Germain wasa na biyu a Champions League da Barcelona a Faransa ba.

Ranar Laraba, kungiyar ta Faransa za ta karbi bakuncin ta Nou Camp, domin buga wasa na biyu na kungiyoyi 16 da suka rage a gasar.

Ranar 16 ga watan Fabrairu Paris St Germain ta doke Barcelona da ci 4-1 a Spaniya a karawar farko, inda Kylian Mbappe ya ci uku rigis a wasan.

Barcelona ta ci kwallonta ta hannun kyaftin Lionel Messi a bugun daga kai sai mai tsaron raga, yayin da Moise Kean na PSG ya zura kwallo a Spaniya.

A wani jawabi da PSG ta fitar ta ce Neymar, wanda ya bar Barcelona ya koma buga gasar Ligue 1 kan mafi tsada a tarihi a 2017 ya ci gaba da yin atisaye shi kadai.

Neymar, wanda ya yi rauni a watan Fabrairu, kan ci karo da cikas na kasa buga wasa a gasar a irin wannan mataki, ko dai ya ji ciwo ko a hukunta shi

Barcelona wadda ba a zura mata kwallo ba a raga a wasa uku a Champions League na bana ta sha kashi a gida a hannun Juventus da kuma PSG.

Ana fargabar watakila Barcelona za ta yi rashin nasara a karo na uku a jere a karon farko a tarihin kungiyar a gasar Turai ko ta Europa ko kuma ta Champions League.