BBC Hausa of Thursday, 4 March 2021

Source: BBC

ICC ta fara binciken laifukan Isra'ilata aikata a yankunan Falasdinawa

Babbar mai shigar da kara ta Kotun da ke kula da aikata laifukan yaki ta duniya ICC, ta fara bincike kan laifukan yaki da aka aikata a yankunan Falasdinawa a hukumance.

Fatou Bensouda ta ce binciken zai duba abubuwan da su ka faru a yankuna kamar na Yamma da Kogin Jordan da Isra'ilar ta mamaye da Gabashin Jerusalem da kuma Zirin Gaza tun 2014.

A watan jiya kotun ta ICC ta yanke hukunci a watan jiya cewa tana iya yanke da hukunci kan yankunan Falasdinawa.

Isra'ila ta ki amincewa da matakin kotun na binciken ayyukan yakin da aka aikata, amma Falasdinawa na yaba ma ta.

Amurka, wadda ita ce babbar kawar Isra'ila, ta bayyana rashin jin dadinta game da matakin kuma ta ce za ta ki amincewa da shi.

Kotun na da hurumin binciken duka laifukan yaki da aka aikata kan kowane dan Adam a yankunan kasashen da su ka rattaba hannu kan dokar da ta kafa ta mai suna Rome Statute.

Isra'ila ba ta taba rattaba hannu kan dokar ta Rome Statute ba, amma kotun ta yanke hukuncin samun hurumin gudanar da binciken ne saboda sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya amince da shigar Falasdinawa cikin kasashen da su ka rattaba hannu kan yarjejeniyar a 2015.

Isra'ila ta kwace yankunan Yammacin Kogin Jordan da Gaza da Gabashin Birnin Kudus a bayan Yakin Gabas ta Tsakiya na 1967. Falasdinawa na son a mayar mu su da iko kan yankunan domin su zama wani bangare na kasar da su ke son kafa ta Falasdinu a nan gaba.