BBC Hausa of Thursday, 4 March 2021

Source: BBC

'Yan bindiga sun sace mutum 60 sun kona garin Ruwan Tofa a Zamfara

Ruwan Tofa na yankin karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara Ruwan Tofa na yankin karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara

Al'ummar garin Ruwan Tofa na yankin karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara a arewa maso yammacin Najeriya, sun gamu da taskun 'yan bindiga, wadanda rahotanni suka ce sun kona rabin garin da dukiya mai dimbin yawa, kuma suka yi awon gaba da mutane fiye da sittin.

Hakan ya auku ne yayin da matsalar satar 'yan makaranta ta fara auka wa daliban makarantun jeka-ka-dawo a garin Runka na jihar Katsina.

Yanzu haka jama'ar garin sun tsere, "matsalar nan ta yi mana nauyi, ko shekaranjiya da jiya ma sun kawo mana hare-haren nan. Sun kone mana gari da motoci da shaguna da gidaje, kusan rabin garin sun kone shi," in ji wani dan garin da muka biye sunansa.

Ya ci gaba da cewa ba a samu asarar rai ba amma 'yan bindigar sun harbi wani kuma yanzu haka yana asibiti a kwance.

"Sun tafi da mata da yara da dama, akwai wani mutum mai mata hudu duk sun tafi da matan nasa ko daya ba a bar masa ba. Sun tafi da wakilin maigari da iyalansa," in ji shi.

Wani da shi ma lamarin ya shafa ya ce an dauke jama'ar gidansa wajen 15 maza da mata da yara, "sun kwashe min buhu 90 na dawa a wata mota.

"Mun nemi daukin jami'an tsaro har sau biyu amma ba su zo ba, sai muka tarwatse daga garin," in ji shi. BBC ta tuntubi rundunar 'yan sndan jihar Zamfara amma ba a samu ji daga gare su ba.

A garin Runka na jihar Katsina kuwa rahotanni sun ce 'yan bindiga ne suka sace wasu daliban makarantar je ka ka dawo.

Wani mazaunin garin ya ce daliban uku ne aka sace kuma duk maza ne a ranar Talatar da ta wuce. "Ba su wuce shekaru 16 ba kuma suna kan hanyarsu ta koma wa gida ne daga makaranta," in ji ganau din.