Vous-êtes ici: AccueilActualités2021 04 22Article 450355

BBC Hausa of Thursday, 22 April 2021

Source: BBC

Man City ta kara bai wa Man United tazarar maki 11

Manchester City ta yi nasarar doke Aston Villa da ci 2-1 a wasan Premier League Manchester City ta yi nasarar doke Aston Villa da ci 2-1 a wasan Premier League

Manchester City ta yi nasarar doke Aston Villa da ci 2-1 a wasan Premier League da suka kara ranar Laraba a Villa Park.

Minti daya da fara wasa, John McGinn ya ci wa Villa kwallon farko, yayin da minti 11 tsakani Phil Foden ya farke kwallon.

Saura minti biyar su tafi hutu ne City ta kara na biyu ta hannun Rodrigo Hernandez.

Kungiyoyin biyu sun karasa karawar da 'yan wasa goma-goma a cikin fili, bayan da aka bai wa John Stones na City jan kati daf da hutu.

Daga baya shima dan kwallon Aston Villa, Matty Cash aka kore shi daga fafatawar daf da komawa zagaye na biyu.

Da wannan sakamakon City wadda take ta daya a kan teburi ta hada maki 77 da tazarar 11 tsakaninta da Man United mai biye da ita.

Ita kuwa Villa tana ta 11 a kasan teburin Premier League da maki 44, bayan wasa 31 da ta yi.

Ranar 25 ga watan Afirilu Manchester City za ta kara da Tottenham a wasan karshe a Caraboa Cup a Wembley.

Ranar Litinin Tottenham ta kori Jose Mourinho ta nada kocin rikon kwarya Ryan Mason, wanda ya fara da nasara a kan Southampton da ci 2-1 ranar Laraba.

Ranar Talata Manchester City ta sanar da fita daga gasar European Super League, bayan da tsarin ya ci karo da suka daga Fifa da Uefa da masu ruwa da tsaki.

Tottenham ma tana daga cikin kungiyoyin Ingila da ta janye daga gasar, bayan Chelsea da Arsenal da Liverpool da kuma Manchester United.