Vous-êtes ici: AccueilActualités2021 03 15Article 449655

BBC Hausa of Lundi, 15 Mars 2021

Source: BBC

Arsenal ta ajiye Aubameyang a benci matakin hukunci

Kyaftin Arsenal Pierre-Emerick Aubameyang Kyaftin Arsenal Pierre-Emerick Aubameyang

An ajiye kyaftin Pierre-Emerick Aubameyang a benci a hukuncin da Arsenal ta yi masa daf da za ta buga wasa da Tottenham ranar Lahadi.

Tun farko an bayyana Aubameyang cikin jerin 'yan wasa 11 da za su buga mata wasan na Premier a Emirates, amma an sauya shi da Alexandre Lacazette.

Koci Mikel Arteta ya fada cewar sun yanke wannan hukuncin ne a matakin ladabtarwa ga dan kwallon tawagar Gabon.

"Muna da tsari da doka da ya kamata kowa ya martaba a kowanne wasa shi ne kawai batun."

"Wannan mataki ne da muka dauka, bayan nazarin abin da ya faru da abin da kyaftin din ya aikata da ta kau muka yanke hukuncin."

Kocin ya kara da cewar: "Muna da 'yan wasa da yawa, muna kuma yin sauye-sauye, kuma muna da 'yan wasan da a shirye suke su buga mana kwallo, kuma hakan nake bukata."