Vous-êtes ici: AccueilActualités2021 05 24Article 450932

BBC Hausa of Monday, 24 May 2021

Source: BBC

Mandzukic zai bar AC Milan saboda yawan jinya

Mario Mandzukic ya sanar zai bar AC Milan, sakamakon raunin da yake ta yi, bayan wata shida da ya yi a kungiyar ta Italiya.

Mai shekara 35 dan kasar Croatia ya koma Milan a matakin wanda bai da kungiya a watan Janairu da yarjejeniyar da zai kare a karshen kakar 2020/21.

''Abin alfahari ne da na buga tamaula a AC Milan - Ina godiya ga mahukuntan kungiyar bisa damar da suka bani da koci da abokan taka leda da suka bani gagarumar gudunmawa.

Dan wasan ya rubuta a kafarsa ta sada zumunta a Instagram ''Na yi farin ciki da muka kai kungiyar gasar Champions League da za a buga a badi gurbin da ya kamace ta - ina yi wa dukkan kowa da kowa fatan alheri''.

Mandzukic ya buga wa Milan wasa 11 a dukkan fafatawa, wadda ta kare Serie A ta bana a mataki na biyu, sai dai dan kwallon ya yi kusan wata biyu yana jinya.

Milan ta karkare kakar bana a mataki na biyu ne, bayan da ta je ta doke Atalanta da ci 2-0 ranar Lahadi a wasan mako na 38 a gasar Serie A.

Juventus wadda ta lashe kofin Serie A tara a bara na bana ya gagareta ta kammala kakar bana a mataki na hudu, bayan da ta je ta ci Bologna 4-1 ranar Lahadi.

Inter Milan ce ta lashe kofin Serie A na bana.