Vous-êtes ici: AccueilInfos du MondeSport2021 04 19Article 450296

BBC Hausa of Monday, 19 April 2021

Source: BBC

Leicester ta kai wasan karshe a FA Cup a karon farko tun 1969

Kelechi Iheanacho ne ya ci wa Leicester kwallon da ya kai ta wasan karshe a FA Cup din Kelechi Iheanacho ne ya ci wa Leicester kwallon da ya kai ta wasan karshe a FA Cup din

Leicester City ta kai wasan karshe a FA Cup a karon farko tun bayan 1969, bayan da ta doke Southampton 1-0 a Wembley ranar Lahadi.

Dan wasan tawagar Najeriya, Kelechi Iheanacho ne ya ci wa Leicester kwallon da ya kai ta wasan karshe a FA Cup din.

An buga karawar ta daf da karshe da 'yan kallo 4,000 a wini bincike da ake yi na ko ya dace a bar magoya baya su shiga sitadiya, bayan da cutar korana ta hadasa koma baya.

An bai wa magoya bayan Leicester da na Southampton na su kason 'yan kallon, sannan aka takaita wanda aka sayar a filin wasa na Wembley.

Kuma wannan ce karawar farko da Leicester City ta buga daf da karshe a FA Cup din tun bayan 1982.

Da wannan sakamakon Leicester karkashin jagorancin Brendan Rodgers za ta buga wasan karshe da Chelsea ranar 15 ga watan Mayu a Wembley.

A ranar Asabar Chelsea ta yi nasara a kan Manchester City da ci 1-0 a fafatawar da suka yi ta daf da karshe a FA Cup din.