Vous-êtes ici: AccueilInfos du MondeGeneral2021 05 11Article 450717

BBC Hausa of Tuesday, 11 May 2021

Source: BBC

Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Sancho, Camavinga, Zakaria, Tomori, Aguero, Bamford, Wilder

Jadon Sancho, dan Ingila kuma dan wasan Borussia Dortmund Jadon Sancho, dan Ingila kuma dan wasan Borussia Dortmund

Manchester United ta daina daukar dan wasan gaba na gefe na Borussia Dortmund, dan Ingila Jadon Sancho, mai shekara 21, a matsayin wanda ta fi son saye, kusan saboda samun abokin wasansa a tawagar kasarsu, Mason Greenwood. (Jaridar Manchester Evening News)

Dan wasan da Arsenal ta fi son saye a bazaran nan shi ne Eduardo Camavinga, mai shekara 18, da ke wasa a tsakiya, a kungiyar Rennes, dan kasar Faransa. (Jaridar Le10 Sport)

Amma kuma duk da haka Gunners din na sha'awar dan wasan tsakiya na Borussia Monchengladbach da kasar Switzerland Denis Zakaria, mai shekara 24. (90min)

Sai dai kuma mai tsaron ragar Jamus Bernd Leno, mai shekara 29, da dan bayan Sifaniya Hector Bellerin, mai shekara 26, na daga cikin 'yan wasa shida da Arsenal din za ta sayar a bazaran nan. (Jaridar Football London)

Wakilin dan wasan tsakiya na Ingila da Aston Villa Jack Grealish ya ce akwai kungiyoyi da yawa da suke sha'awar sayen dan wasan mai shekara 25. (SNTV daga jaridar Birmingham Mail)

AC Milan na son daukar dan baya Fikayo Tomori, mai shekara 23, wanda a yanzu yake zaman aro a kungiyar ta Italiya, daga Chelsea, zaman dindindin. (Jaridar Goal)

Sayen dan wasan gaba har yanzu shi ne abin da Barcelona ta fi ba wa fifiko, inda take sa ran samun Erling Braut Haaland, na Borussia Dortmund dan kasar Norway mai shekara 20, sai kuma Sergio Aguero, na Manchester City, dan Argentina mai shekara 32 a matsayin wani zabin da idan ta rasa Erling. (Jaridar Mundo Deportivo)

Tottenham Hotspur za ta sayar da dan bayanta Davinson Sanchez, dan kasar Colombia mai shekara 24, a bazaran nan. (Jaridar Football Insider)

Chris Wilder na daga cikin sabbin masu horarwa da West Bromwich Albion za ta yi zawarci idan Sam Allardyce ya bar kungiyar bayan faduwarsu daga gasar Premier. (Sky Sports)

Newcastle United na son daukar dan wasan gaba na gefe Joe Willock zaman dindindin, a bazaran nan bayan da dan wasan na Ingila mai shekara 21, wanda Arsenal ta ba ta aronsa ya taka rawar gani. (Talksport)

Kungiyoyin Newcastle da Crystal Palace da Fulham da kuma Watford na sa ido sosai a kan tsohon dan wasan gaba na Chelsea Gael Kakuta.

Kakuta mai shekara 29 dan Faransa amma asalin Jamhuriyar Dumokuradiyyar Kongo a yanzu yana zaman aro ne a Lens daga kungiyar Amiens, ita ma ta Faransa. (Jaridar Mail)

Wolverhampton Wanderers da Watford na sha'awar sayen dan wasan gaba na Senegal Mbaye Diagne. Dan wasan mai shekara 29 a yanzu aro a West Brom daga Galatasaray ta Turkiyya. (Jaridar Football Insider)

Kungiyoyin gasar kasa da Premier ta Championship Stoke City da QPR na son dan wasan baya na gefe na Aston Villa Neil Taylor. Dan bayan na Wales mai shekara 32 zai kasance bas hi da kungiya a bazaran nan. (Jaridar Sun)

Dan wasan gaba na Leeds United, dan Ingila Patrick Bamford, mai shekara 27, ya tsawaita kwantiraginsa da kungiyar a bazarar bara ba tare da an sani ba. (Jaridar The Athletic )