Vous-êtes ici: AccueilInfos du MondeGeneral2021 05 10Article 450690

BBC Hausa of Monday, 10 May 2021

Source: BBC

Arsenal ta nutsa West Brom zuwa Championship

Cocin West Ham, Sam Allardyce Cocin West Ham, Sam Allardyce

West Brom za ta koma Championship a badi, bayan da ta sha kashi da ci 3-1 a hannun Arsenal a gasar Premier da suka kara ranar Lahadi a Emirtaes.

Tun kan hutu Gunners ta zuba kwallo biyu a ragar West Brom ta hannun Emile Smith-Rowe da kuma Nicolas Pepe.

Bayan da suka yi hutu suka koma zagaye na biyu ne West Brom ta farke daya ta hannun Matheus Pereira, daga baya Arsenal ta kara na uku hannun Willian Borges Da Siva.

Saura wasa uku-uku a karkare kakar bana, Arsenal tana mataki na tara da maki 52, har yanzu da aiki a gabanta a neman gurbin shiga gasar Zakarun Turai ta badi.

Ranar Alhamis Villareal ta yi waje da Gunners daga Europa League da ci 2-1 gida da waje, kuma tsohon kocinta Unai Emery ne ya yi wannan bajintar zuwa wasan karshe.

Wannan shi ne karon farko da Sam Allardyce ya fadi daga gasa a matakin mai horar da tamaula a Premier League.

Kocin mai shekara 66 ya karbi aiki a hannun Slaven Bilic a cikin watan Disamba a lokacin da kungiyar ke mataki na 19 a kasan teburin Premier League.

Allardyce ya taba ceto kungiyoyi daga faduwa daga Premier da suka hada da Blackburn Rovers da Sunderland da kuma Crystal Palace.

Wasa hudu kacal ya yi nasara daga 22 da ya ja ragamar kungiyar a kakar bana a gasar Premier League.

Wannan shi ne karo na biyar da West Brom ke faduwa daga gasar Premier League, kam,ar yadda Norwich City keda tarihin barin gasar karo biyar.