Vous-êtes ici: AccueilInfos du MondeCulture2021 04 20Article 450333

BBC Hausa of Tuesday, 20 April 2021

Source: BBC

Shugaban kasar Chadi Idriss Derby ya mutu

Rundunar sojin Chadi ta ce Shugaban kasar Idriss Derby ya mutu sakamakon raunukan da ya ji a fagen daga.

A halin yanzu dai Chadi tana fafatawa da mayakan da ke tawaye wadanda suka kaddamar da hari kan babban birnin kasar N'Djamena.

Ana sa ran Shugaba Idriss Derby zai lashe zaben shugaban kasar karo na shida bayan zaben da aka gudanar a watan Afrilu.