Vous-êtes ici: AccueilActualitésRégional2021 04 09Article 450121

BBC Hausa of Friday, 9 April 2021

Source: BBC

Arsenal ta yi sakaci a Europa League ranar Alhamis

Arsenal ta ci kwallon ne ta hannun Nicolas Pepe saura minti hudu a tashi Arsenal ta ci kwallon ne ta hannun Nicolas Pepe saura minti hudu a tashi

Kungiyar Arsenal ta tashi wasa 1-1 da Slavia Prague a karawar farko a quarter final da suka fafata a Emirates ranar Alhamis.

Arsenal ta ci kwallon ne ta hannun Nicolas Pepe saura minti hudu a tashi daga wasan, kuma daga baya ya shiga karawar.

Sai dai kuma Slavia Prague ta farke kwallon daf da lokaci zai cika ta hannun Thomas Holes, kuma hakan na nufin sai a wasa na biyu za a fitar da gwani kenan.

Arsenal za ta ziyarci Prague a wasa na biyu na quarter final ranar Alhamis.

Gunners na bukatar lashe kofin Europa League na bana, idan har tana son buga gasar Zakarun Turai a badi.

Arsenal din tana ta 10 a teburin Premier League da maki 42 a babna, kuma wannan matakin ba zai kai ta Europa League a badi ba.

Ranar Lahadi 10 ga watan Afirilu Arsenal za ta ziyarci Sheffield United a gasar Premier League.