Vous-êtes ici: AccueilActualitésRégional2021 05 11Article 450732

BBC Hausa of Tuesday, 11 May 2021

Source: BBC

Yadda al'adar koya wa yara sana'a ta samar da attajirai a kabilar Igbo

Al'ummar Igbo sun yi fice a matsayin 'yan kasuwa saboda tsarin koyar da sana'o'in Al'ummar Igbo sun yi fice a matsayin 'yan kasuwa saboda tsarin koyar da sana'o'in

Al'ummar Igbo sun yi fice a matsayin 'yan kasuwa a wani bangaren saboda tsarin koyar da sana'o'in hannu sanadin yaki, kamar yadda wakilin BBC a Legas Chiagozie Nwonwu ya rubuta.

Onyeka Orie dan shekara 28 cike da murmushi a fuskarsa yana farin ciki da bunkasar shagonsa na sayar da kayan wayar hannu a kasuwar Computer Village da ke Legas.

Tsohon mai gidansa ne ya ba shi shagon da duk wani abu da ke cikinsa bayan da Mr Orie ya yi masa aiki ba tare da biyansa ba na tsawon shekaru yana koyon sana'a.

"Na yi aiki da mai gidana tsawon shekara 8. Shi ya ba ni wannan shagon. Na yi shekara hudu ina kula da shagon kafin ya mallaka min shi, ban yi tunanin haka za ta faru ba," in ji Mr Orie yana mai cike da murna.

Mr Orie wanda iyayensa manoma ne a kudu maso gabashin Najeriya ya ce ya tashi cikin talauci saboda iyayensa ba su iya ba shi ilimin da yake bukata ba don samun aiki mai kyau a kasar da rashin aikin yi ya yi kamari, har ma ga wadanda ke da karatun digiri.

Bayan makarantar sakandare ne ya shiga sahun matasan Igbo masu son koyon sana'oi karkashin wani tsari mai suna "Igba Boi" - inda matasa mafi yawansu maza ke barin iyalansu domin zama tare da yan kasuwar da suka shahara.

Ana sa ran matasan za su yi wa masu koya musu sana'o'in hidima, suna yi musu komai - har da wanke mota da zuwa aiken gida. Ta haka ne su matasan ke kara samun kwarewa kan sana'o'in sannan ana koya musu yadda za su tafiyar da kasuwanci.

Ana kuma basu abinci da kuma wajen zama.

A karshen wani dan lokaci da aka diba, sai mai gidansu ya ba su jari domin soma kasuwancinsu.

Tsarin koyon sana'o'in na Igbo ya samo asali ne tun daga shekarun da Najeriya ta yi fama da yakin basasa, in ji Ndubisi Ekwekwe, wani Farfesa dan Najeriya wanda ake shirin wallafa rubutun da ya yi kan tsarin a mujallar Harvard Business Review cikin wannan watan.

Al'ummar Igbo wandanda yakin basasar na 1967 zuwa 1970 ya fi shafa sun farfado da matsayinsu na tattalin arziki cikin shekara biyu kawai.

Hakan ya faru ne duk da cewa gwamnatin Najeriya ta rufe asusun ajiyar bankin akasarin al'ummar Igbo. A lokacin gwamnatin ta ba su dala 28 a matsayin jari.

Wata kungiya mai suna Peoples Club da aka kafa a garin Aba a shekarar 1971 na da hannu a yadda aka kafa tsarin ba da horon sana'o'in,

A tsarin, ana girmama batun da al'ummar Igbo ke cewa "kada ka bar dan uwanka a baya."

"Kungiyar ce ta tsara yadda al'ummar Igbo za su fita daga halin da suka shiga sanadin yakin sannan su ci gaba da rayuwa," in ji Benecict Okoro, wanda ya kirkiri gidauniyar al'adun gargadjiya ta Odinala.

"Wannan shi ne asalin Igba Boi a kabilar Igbo."

Galibi ana aiwatar da tsarin ne kan maza da samari saboda iyalai ba su cika barin yayansu mata su zauna tare da yan kasuwa ba tsawon shekara biyar domin koyon sana'oi.

A maimakon haka, mata suna koyon kasuwanci ne ta hanyar biyan kudi domin a koya musu sana'oi cikin wata shida zuwa shekara daya.

'Ban tashi da komai ba bayan shekara bakwai'

Fitattun yan kasuwa a Najeriya irinsu Innocent Chukwuma na kamfanin kera motoci na Innoson da Cosmas Maduka na kamfanin Coscharis suna daga cikin wadanda suka ci gajiyar tsarin.

A wata hira da BBC Igbo cikin shekarar 2019, Mr Maduka ya ce naira 200 da mai gidansa ya ba shi bayan ya gama samun horon a 1976 ne ya ba shi kafar samun nasara a kamfaninsa na miliyoyin kudi.

Ana kuma iya ganin nasarar tsarin a biranen da ke Kudanci irinsu Onitsha da Aba da Nnewi inda 'yan kasuwa ke zuwa cin kasuwa daga sassan Yammacin Afirka.

Amma akwai wasu da ke sukar tsarin saboda ya dogara ne kan yadda mai koyar da sana'ar ya kula da wadanda ya horar bayan koya musu.

Ndubuisi Ilo, wanda yake da shagon sayar da kayan gyaran motoci a Ladipo da ke Legas ya ce ba abin da aka ba shi bayan ya shafe shekara bakwai.

"Wata rana mai gidana ya kira ni ya fada min cewa ba zai iya biya na kudi ba. Ya yi min addu'a kuma ya nemi na fara gwagwarmayar tsayawa da kafata.

Da farko abin bai zo min ta sauki ba har ma ta kai ina kwana cikin motoci amma a yanzu idan na tuna na kan yi murmushi ne, " in ji shi.

Duk da haka ba ya kallon tsawon lokacin da ya shafe a matsayin ba ta lokaci saboda ya yi amfani da ilimin wajen gina kasuwancinsa.

"Wasu yan kasuwar ba sa son kulla yarjejeniya saboda kudin da ake kashewa wajen kafa kasuwanci ga wanda ya koyi sana'a.

"Wasunsu na zargin wandanda suka koyi sana'ar da yi musu sata ko kuma wani abin da zai sa su kawo karshen yarjejeniyar," in ji Mr Ilo.

Yarjejeniyar Igba Boi da baki ake yinta kuma a mafi yawan lokuta, su ma su koyon sana'o'in ba su da wani zabi musamman idan mai gidan nasu ya saba yarjejeniyar.

Tun da yawancin yan kasuwar suna da alaka ta jini, yan uwa suna kokarin shiga tsakani domin sasantawa amma idan ba su yi nasara ba, sai kakanni su sa baki domin warware lamarin.

A wasu lokutan ana warware lamarin cikin sauki, wasu lokutan kuma ba haka abin yake ba, sai kuma a bar mai koyon sana'ar yana bilunbituwar kula da kansa bayan shafe shekaru ana morarsa.

'Misali ga Afirka'

Gidauniyar Mr Okoro na neman a inganta tsarin Igba Boi domin rage yawan mutanen da ke shiga wani hali sanadin rashin mutunta yarjejeniyar.

"Gina cikakken tsari zai zama akwai tsarin doka kuma ba zai zama kawai tsakanin yan kasuwar da kuma mai koyo ba da yan uwansa, za a ma iya ba da takardar shaidar kammala koyon sana'oin," in ji shi.

Gidauniyar na diba yadda za ta inganta tsarin na Igba Boi domin matsalolin da ake samu na saba yarjejeniyar.


Mista Ekweke ya lura cewa taimaka wa abokan hamayyar kasuwanci ya saba wa tunanin jari-hujja na gargajiya amma ya shiga zuciyar wannan tsarin, wanda galibi yana aiki sosai ga duk wanda abin ya shafa.

"(Masanin tattalin arziki) Adam Smith ya yi imanin cewa samun nasara a harkokin kasuwanci ya kunshi tabbatar da gogayya da abokan hamayya, amma wannan tsarin ya dogara ne da kawo karin mutane cikin kasuwancin," in ji shi.

Ya ce yana son gabatar da tsarin koyon kasuwanci na tsarin a matsayin nazari ga duniya yayin da ake ci gaba tattaunawar tsarin jari-hujja na masu ruwa da tsaki, ba wai kawai jari-hujja na masu hannun jari ba'"

'Ya fi mallakar digirin jami'a'

Alƙalumman rashin ayyukan yi a Najeriya ya nuna kashi 33 da ke neman aikin sun kasa samu. Yawancinsu waɗanda suka kammala digirin jami'a ne

Mr Orie ya ce tsarin tallafi ya fi inganci fiye da sauran ire-irensa da suka tafi jami'a yin karatu.

Ya ce yana tunanin ɗauko wani matashi daga ƙauye domin kayon kasuwanci a karkashinsa.

Yawancin ire-irensa yanzu suna ɗaukar mai tsaron shago maimakon yin amfani da tsarin Igba Boi.

Amma Mr Illo ya ce makomar tsarin wanda ya samar da irinsa da wasu miliyoyi yana nan.

"Idan har akwai kasuwanni da ƴan kabilar Igbo ƴan kasuwa, za a samu masu koyon kasuwancin," in ji shi.