Vous-êtes ici: AccueilOpinionsActualités2021 05 31Article 451072

BBC Hausa of Lundi, 31 Mai 2021

Source: BBC

Champions League: An bayyana 'yan wasa 11, amma ba Kante

Chelsea ta lashe Champions League bayan ta doke Man City a Porto Chelsea ta lashe Champions League bayan ta doke Man City a Porto

Ranar Asabar Chelsea ta lashe Champions League, bayan da ta doke Manchester City 1-0 a Porto, Portugal.

Mai tsaron bayan Chelsea, Cesar Azpilicueta shi ne ya yi kyaftin kuma shi ne ya daga kofin Champions League na bana, kuma na biyu da Chelsea ta dauka a tarhi.

Azpilicueta dan kwallon tawagar Sifaniya shi ne kadai cikin 'yan wasa 11 da suka taka rawar gani a gasar Zakarun Turai ta bana.

Kungiyar Chelsea tana da 'yan kwallo a ciki da suka hada da Edouard Mendy da Azpilicueta da Antonio Rudiger da kuma Jorginho.

Ita kuwa City tana da 'yan wasa da suka hada da Kyle Walker da Ruben Dias da Ilkay Gundogan da kuma Phil Foden.

Sai dai cikin fitattun 'yan wasan Champions League na bana ba N'Golo Kante wanda shi ne ya zama zakakurin dan wasa a karawar da Chelsea ta yi da Real Madrid gida da waje.

Fitattun 'Yan wasa 11 a gasar Champions League ta bana:

Mai tsaron raga:

  • Edouard Mendy


  • Masu tsaron baya:

  • Kyle Walker (Man. City)


  • Antonio Rudiger (Chelsea)


  • Ruben Dias (Man. City)


  • Cesar Azpilicueta (Chelsea)


  • Ilkay Gündoğan (Man. City)


  • Jorginho (Chelsea)


  • Phil Foden (Man. City)


  • Masu cin kwallo:

  • Mohamed Salah (Liverpool)


  • Erling Haaland (Dortmund)


  • Kylian Mbappé (Paris Saint-Germain)