Vous-êtes ici: AccueilOpinionsActualités2021 03 09Article 449559

BBC Hausa of Mardi, 9 Mars 2021

Source: BBC

Coronavirus: Isra'ila ta soma yi wa Falasɗinawa rigakafin korona

Firimiyar Isra'ila Benjamin Netanyahu Firimiyar Isra'ila Benjamin Netanyahu

Ƙasar Isra'ila ta fara yiwa dubban Falasdinawa allurar rigakafin korona.

Wadanda ke da lasisin aiki na Isra'ila za su karbi allurar rigakafin Moderna a wuraren tsallakawa zuwa gabar yammacin kogin Jordan, da kuma a matsugunan Yahudawa.

Masu rajin kare hakkin dan adam sun yi kira ga Isra'ila ta kara himma sosai, suna masu cewa nauyin yi wa alatsinawa rigakafin ya rataya ne a wuyanta.

Akalla Falasdinawa miliyan uku basu samu rigakafi ba a gabar yammacin kogin Jordan, inda yawan masu kamuwa da cutar ke karuwa.

Ita dai Isra'ila ta musanta cewa ita ke da alhakin yi wa Falatsinawan rigakafi.

Yanzu haka ta yiwa fye da rabin yan kasarta allurar, kuma tuni tattalin arzikinta ya soma farfadowa.