Vous-êtes ici: AccueilCulture2021 05 07Article 450660

BBC Hausa of Vendredi, 7 Mai 2021

Source: BBC

Matsalar Tsaro: Kawunan Malaman addinin Musulunci sun rabu kan biyan kudin fansa

Hagu zuwa dama: Skeikh Gumi, Sheikh Maqari, Sheikh Bello Yabo da Sheikh Yusuf Asadus-Sunna Hagu zuwa dama: Skeikh Gumi, Sheikh Maqari, Sheikh Bello Yabo da Sheikh Yusuf Asadus-Sunna

Muhawara ta kaure a tsakanin wasu malaman addinin Musulunci a Najeriya game da halasci ko haramcin biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutane a kasar.

Hakan na faruwa ne a yayin da masu garkuwa da mutanen suke ci gaba da satar jama'a suna neman a biya su miliyoyin kudi kafin su sake su, a wasu lokutan kuma sukan kashe su ko da an biya kudin.

Kodayake babu ingantattun alkaluma na yawan mutanen da aka sace da zummar biyan kudin fansa musamman a yankin arewa maso yammacin Najeriya, sai dai bayanai sun tabbatar da cewa an sace dalibai fiye da 800 daga watan Disambar da ya wuce zuwa yanzu. Kuma rahotanni sun nuna cewa an bayar da kudin fansa kafin a saki wasu daga cikinsu.

Baya ga dalibai, masu garkuwa da mutane suna ci gaba da karbar makudan kudin fansa kan daidaikun jama'a.

Ra'ayoyin mahukunta sun sha bamban game da yin sulhu ko kuma bayar da kudin fansa ga wadannan 'yan bindiga da ke garkuwa da mutane

Daya daga cikin masu adawa da biyan kudin fansa ga 'yan bindigar shi ne Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, wanda ke ganin bayar da kudin fansar daidai yake da karfafa gwiwar masu aikata wanna munnuna aiki.

Sai dai a nasa bangaren, Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara na ganin yana da kyau a yi sulhu da masu garkuwa da mutanen.

Su kansu malaman addini suna da mabambanta ra'ayi game da biyan kudin fansa.

Yayin da wasu ke cewa haramun ne a rika biyan masu satar mutanen kudin fansa, wasu kuwa cewa suke yi hakan ya halasta. Ga ra'ayoyin wasu daga cikinsu:

Sheik Ibrahim Maqari

Wannan muhawara ta biyo bayan kalaman da fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na kasar, Farfesa Ibrahim Maqari, ya yi cewa biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutane haramun ne a Musulunci.

Malamin, wanda shi ne mataimakin babban limamin Masallacin Juma'a na Abuja, ya ce Musulunci ya hana mabiyansa bayar da kudin fansa ga makiya da ake yaki da su.

Farfesa Maqari, wanda ya bayyana haka lokacin Tafsirin da yake gabatarwa a watana azumin Ramadana, ya kara da cewa biyan kudin fansa zai karfafa gwiwar masu garkuwa da mutane da kuma ba su karin kudi da za su sayi makamai don ci gaba da kai hare-hare.

"Tun da Allah (SWT) ya haramta biyan kudi ga makiyi wanda yake yaki da kai, domin kada ka kara masa karfi, don haka biyan kudin fansa domin a saki wanda aka yi garkuwa da shi haramun," in ji shi.

Malamin ya ambato Hadisin da wani mutum ya je wurin Manzon Allah yana tambayarsa kan abin da zai yi idan wani ya yi yunkurin ya yi masa fashi da makami, inda Annabi (SAW) ya umarce shi da ya yake shi.

Sheik Bello Yabo

Shi ma Sheik Bello Yabo, wani malamin addinin Musulunci ne da ya goyi bayan fatawar ta Sheik Ibrahim Maqari game da haramcin biyan kudin fansar, inda ya yi kira ga jama'a da kada su sake su biya kudin fansa yana mai cewa duk wanda aka kashe saboda dukiyarsa, ya yi shahada.

Malamin, wanda shi ma ya bayyana hakan a yayin gudanar da Tafsirinsa na watan azumin Ramadan, ya ce bai ga dalilin da zai sa a rika kara wa 'yan ta'adda karfin gwiwa ba wajen biyan su kudin fansa bayan sun sace mutane.

"Ina mamaki wadanda suka sace mutane su ce a kawo miliyan uku, a kawo miliyan biyar, jiki na rawa sai ka ga an hada an kai musu, wai ba ku kyale su ne? Duk wanda aka dauka kada ya bayar da ko kwabo a kashe shi!" in ji shi.

Sheik Yabo ya kuma ce bayar da kudin fansar da ake yi ne ta sa 'yan ta'addar ke ci gaba da sace-sacen jama'a saboda suna kara samun karfin gwiwa.

"Don haka ko da Allah ya sa aka dauke ni, ban yarda ko magana a yi ba, wanda duk ya yarda aka bugo masa waya a tattauna da shi kan a fanshe ni, idan na fito sai mun yi fada da shi," a cewarsa.

Ya kuma kara da cewa: "Kuna daukar kudi kuna bai wa azzalumai, mashaya, wadanda ko sallah ba sa yi, kuna kara musu karfi ya za a yi su daina?".

Malamin ya bayar da shawara cewa duk wanda masu satar mutane suka dauke kuma suka kuma bugo waya suna neman kudin fansa su kyale su kada su bayar.

Ya ce ta hakan ne zai sa masu aikata irin wannan ta'asa su daina idan suka ga sun daina samun komai bayan sun sace mutanen.

''Idan aka dauki mutum kada a basu ko kwabo, ku gani idan ba su daina ba, don haka duk wanda aka dauki wani na shi ya ce musu ya yafe su kashe shi ya yi shahada kawai,'' in ji malamin.

Sheik Ahmed Mahmud Gumi

Amma kuma a nasa bangaren, fitaccen malamin nan Sheik Ahmed Gumi ya bayar da fatawa cewa ya halasta mutum ya biya kudi ya fanshi kansa a duk lokacin da rayuwarsa ta shiga cikin hadari.

Ya ce haramta biyan kudin fansar shi kansa haramun ne a Musulunci.

''Idan irin wadannan mutane suka ce sai ka kawo kudin fansa don ka fanshi kanka babu komai ka yi abin da shari'ar Musulunci ta yarda da shi", in ji Sheik Gumi.

Ya kara da cewa: "Ba ma kudi ba, idan an tsare ka aka ce ranka za a kashe amma sai ka kafirta, ka yarda ka kafirta amma a baki. Allah na kama ka ne idan akwai kafircin a zuciyarka''.

Malamin ya ce duk abin da aka ce kada a yi idan lalura ta zo kana iya aikatawa don ka samu ka tsira da rayuwarka.

Ya kuma ja hankalin sauran malamai game da abinda ya ce bayar da fatawa kan abubuwan da ba sa cikin hurumin addinin Musulunci.

Ya ce: ''Ina yi wa wasu malamanmu gargadi su daina yin fatawa a inda ba muhallinta ba ne, bai kamata idan an yi garkuwa da mutane ba, mutum ya fanshi kansa sannan a ce haramun ne."

Sheik Ahmed Gumi ya kuma bayyana cewa idan za a yaki ta'addanci shugabanni ne da dakaru ya kamata su sadaukar da rayukansu amma ba wanda aka sace ba.

''Shugabanni su ya kamata su sayar da ran su ba wanda aka kama ba, ga tsohon shugaban kasar Chadi Idris Derby ai ya sadaukar da ransa ne wajen yaki da 'yan ta'adda, to haka ake yaki da ta'addanci" in ji malamin.

''Me ya sa wasu malamai a kullum suna son cutar da wasu bayan Allah don kawai suna son su dadadawa wasu?''

Malami ya kara jaddada cewa duk wanda ya fanshi kan sa lokacin da ya shiga cikin matsala babu komai a addinin Musulunci.

''Ita kuma hukuma idan ta san ba za ta iya biyan kudin fansa don ceton rayukan jama'arta ba to ta yi kokarin yadda za ta kare rayukan mutane daga fadawa cikin matsala," ya ce.

''Ko da hukuma ce ta bayar da kudi Allah ba zai kama ta da wani laifi ba, wajibinsu ne, ya fi sauki a bayar da kudi a ceci rayukan mutane''.



Sheik Musa Yusuf Asadus-Sunna

Haka shi ma Sheik Musa Asadun-Sunna, wani fitacce malami ne da shi kuma ya mayar da martani ne kan fatawar da Sheik Ibrahim Maqari ya yi a kan cewa biyan kudin fansa haramun ne.

Sheik Asadus-Sunna dai ya ce biyan kudi fansa ga masu sace mutanen bai zama haramun a tun da addinin Musulunci ya bayar da damar mutum ya fanshi kansa a lokacin da ya shiga matsala.

Ya ce musamman ma da yake matsalar sace-sacen jama'a don neman kudin fansa na ta'azzara ta kuma fadada a kusan sassan jihohin kasar.

''Kada ku manta ba fa daga wajen Najeriya ake tattaunawa da wadannan 'yan ta'adda ba, suna cikin Najeriya ana tattaunawa da su za a kawo musu kudi, sannan suna cewa gwamnan Kaduna ya ce idan wani na shi ya fita aka kama shi,'' in ji malamin.

Ya kuma ce idan matsala na fara da kadan-kadan lokaci ne da ya kamata a ce an dauki matakan dakile ta tun kafin ta kara girma kamar halin da aka shiga a yanzu.

''Lokacin da ta fara da kadan-kadan ne a arewacin Najeriya, shin ya kamata a ce an bari har sai matsalar ta kawo yadda take a yanzu? Amana ce malamai Allah ya dora mana mu rika fadakarwa ko a karba ko kada a karba,'' in ji Sheik Asadus-Sunna.

''Tun a baya ya kamata a ce an astahi an shawo kan matsalar yanzu tagama ko ina.''

Malamin ya kara jaddada adawarsa da fatawar ta Sheik Maqari game da haramcin da ya ce biyan kudin fansa na da shi, da cewa kowa ya san hakkin tsaro ya rataya a wuyan hukumomi, su Allah zai tambaya, don haka batun cewa mutum ya yi shahada kada ya biya kudin fansa ba daidai ba ne.

''Ya za ka cewa mutane su yi shahada? Idan haka ne malaman da ke da ra'ayi irin na Maqari sai su fito su nemi gwamnati su yi fatawa ta halattawa kowa sayen makaman da za kare kan sa,'' in ji shi.

Sheik Assadu ya ci gaba wajen kalubalantar Sheik Maqari a kan cewa adddinin Musulunci bai haramta wa mutum ya fanshi kan sa ba a lokacin da bukatar hakan ta taso. don haka yana da ja game da batun na Maqari.

Ya ce: "Saboda haka irin wadannan abubuwa - kun ji na farko ya ce haramun ne, na biyu ya ce kada ka bayar da kudin fansa, na uku ya ce ka yake shi, ai maganar ka yi yaki sai idan kana da makami.

Duk malaman da yake ganin kada a bayar da kudin fansa, to ku fito ku ce gwamnati ta yi fatawa ta halasta wa kowanne dan Najeriya mallakar makami don tunkarar matsalar tun da ita ta kasa yin komai a kai."

Sheik Assadus-Sunna din ya kuma ce a duk lokacin da za ka shiga cikin wata matsala a bayar da wani abu a karbe ka, wannan Allah ya kawo shi a matakai daban-daban.

"Maganar fansar nan ko a wajen yaki ne aka kama fursunan yaki akan yi musanya tsakanin abokan gaba, ko kuma a bayar da kudi a karbe su, duk wannan ya halarta,'' in ji malamin.