Vous-êtes ici: AccueilCulture2021 05 27Article 451000

BBC Hausa of Thursday, 27 May 2021

Source: BBC

Kano Pillars ta sake dare teburin Firimiyar Najeriya

Kano Pillars ta yi nasarar doke Nasarawa United da ci 1-0 Kano Pillars ta yi nasarar doke Nasarawa United da ci 1-0

Kano Pillars ta yi nasarar doke Nasarawa United da ci 1-0 a wasan mako na 23 da suka fafata a gasar cin kofin Firimiyar Najeriya ranar Laraba.

Pillars ta ci kwallon ta hannun Auwalu Ali Mallam a minti na 25 da fara tamaula, kawo yanzu dan wasan ya ci kwallo hudu ya kuma bayar da shida aka zura a raga.

Da wannan sakamakon Pillrs ta hada maki 44, bayan buga karawar mako na 23.

Sakamakon wasannin mako na 23 da aka kara ranar Laraba:

  • Kwara United 1-1 Rivers United


  • Dakkada 2-1 FC Ifeanyiubah


  • Kwara United 1-1 Rivers United


  • Warri Wolves 1-0 Lobi Stars


  • Adamawa United 1-0 Katsina United


  • Sunshine Stars 0-0 Mountain of Fire and Miracle


  • Ranar 27 ga watan Mayu za a yi wasa biyu:

  • Enugu Rangers International da Jigawa Golden Stars


  • Abia Warriors da Akwa United


  • An kuma dage karawa tsakanin Heartland da Plateau United da ya kamata a fafata ranar Laraba.