Vous-êtes ici: AccueilActualitésActualités Criminelles2021 04 29Article 450479

BBC Hausa of Thursday, 29 April 2021

Source: BBC

Matsalar tsaro: Bukatar Buhari kan rundunar Amurka tamkar dawo da mulkin mallaka ne - Shehu Sani

Tsohon ɗan majalisar Najeriya Sanata Shehu Sani Tsohon ɗan majalisar Najeriya Sanata Shehu Sani

Tsohon ɗan majalisar Najeriya Sanata Shehu Sani ya ce yana adawa da tsarin dawo da hedikwatar rundunar sojoji masu kula da Afirka wato AFRICOM zuwa nahiyar daga mazauninta da ke Jamus.

Sanata ya bayyana hakan ne bayan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga Amurka domin mai do da rundunar Afirka saboda matsaloli na tsaro.

Gwamnatin ƙasar dai ta ce kiran wani sauyin matsayi ne ga Najeriya wadda a baya ta riƙa nuna adawa kan yadda ƙasashen yamma ke kafa sansanoninsu a nahiyar Afirka. Sai dai yanzu matsalolin tsaron da ake fama da su, sun sanya ganin fa'idar kawo rundunar sojojin na Amurka.

Amma wasu ƴan adawa irinsu Shehu Sani sun ce kiran dawo da hedikwatar rundunar Amurkan ba mafita ba ce, don kuwa matakin zai iya buɗe ƙofa ga wani sabon salon mulkin mallaka da kawo sojojin ƙasashen yamma su zo su karkasa ƙasashe.

'Rundunonin ƙetare ba su ne mafita ba'

Sanatan ya ce da zaran an buɗe irin wannan ƙofa to su ma sauran rundunonin ƙasashen masu karfi irinsu Rasha da Burtaniya da Faransa harta Isra'ila da Iran da Saudiya za su shigo.

Yana mai cewa, "kafa irin wannan hedikwatar na buɗe ƙofa ga ƙulla sauye-sauye a gwamnati da tilastawa gwamnatocin Afirka kan wasu ra'ayoyi kuma fitar su akwai wahala".

"Abin kunya ne a ce har yanzu ƙasashen Afirka na gayyatar turawa duk da shekarun da aka kwashe na daƙile mulkin mallaka."

Shehu Sanu ya ce muddin irin waɗanan rundunoni suka shigo fitarsu akwai wahala, domin maganar ta wuce na tsaro, za ta haifar da gasa ne tsakanin su.

A cewar sanata baya ganin zuwa ƙasashen yamma zai kawo karshen matsalolin da ake gani na tsaro, kawai hadin-kai ake bukata da kafa rundunar tsaro ta Afirka domin yakar matsalolin tsaro.

Sai dai sanata ya ce akwai bukatar neman taimakon kuɗaɗe da kayan yaƙi wajen cimma waɗannan burukan.

Sharhi

Matsalar tsaro dai a ƙasashen afirka na sake tabarbarewa musamman a yankunan Sahel da tsakiyar Afirka.

A Najeriya lumura ba su sauya ba, haka zalika a kulum labarin tsaron ake musamman a satukan baya-bayanan da hare-hare suka yawaita.

Ƙungiyiyon kare hakkin bil adama irinsu na cewa gwamnatin Najeriya ta nuna abin da kawai za a iya kira tsagwaron rashin iya mulki, kuma ta gaza sauke nauyinta na kare rayukan al'ummarta da kawo ƙarshen taɓarɓarewar tsaro da ke ƙaruwa.

Ta ce rashin kataɓus ɗin hukumomi ya sa aikata laifuka da gadara na ci gaba da haɓaka kuma kashe-kashe na bazuwa a sassa da dama na ƙasar.

A cewarta lamarin ya ta'azzara raɗaɗi a zukatan al'ummomin da, da ma ke rayuwa cikin fargaba ta hari.

Gwamnatin Buhari dai a koda yaushe na iƙirarin cewa tana yakar ƴan bindiga da ke sukurkuta lamuran tsaro, sai dai masana na sake jadada cewa babu kayan yaki a hannun jami'an tsaro da ya kamata su kare kasar da dukiyoyi.