Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 25Article 450943

BBC Hausa of Tuesday, 25 May 2021

Source: BBC

Mun amince a kirkiro 'yan sandan jihohi – Wakilan Kano

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje

Ƙungiyoyin fararen hula a jihar Kano da sauran masu ruwa da tsaki sun ce a shirye suke su ga an kirkiro 'yan sandan jihohi a Najeriya - batun da yawanci jihohin kudancin kasar ke fafutukar ganin an yi, wanda kuma jihohin arewaci galibi ba sa goyon baya.

Kungiyoyn sun bayyana haka ne a wani taron tattara shawarwarin yan jihar ta Kano a wani ɓangare na shirin tunkarar zaman sauraren jin bahasin al'ummar ƙasa kan yi wa tsarin mulkin Nijeriya garambawul.

Ya ce taron ya ba da shawara kan yadda za a rika tafiyar da al'amuran yan sandan jihohi ta yadda gwamnoni ba za su rika yi musu katsalandan ba.

Ranar Laraba ne dai za a fara zaman sauraren bahasin a cibiyoyi 12 da aka keɓe na Najeriya, inda 'yan majalisun tarayya za su karɓi shawarwari da buƙatun jama'ar ƙasar game da aikin yi wa tsarin mulkin 1999 gyaran fuska.

Ibrahim Abdullahi Wayya, shugaban kare Gamayyar ƙungiyoyin fararen hula a Kano ya shaida wa BBC cewa a zaman da suka yi da farko, sun karbi ra'ayoyin mutane da dama inda masana suka fayyace wa mahalarta yadda al'amura suke a kundin tsarin mulkin.

"An samu masana daga jami'a da kungiyar dattawan Kano da majalisar malamai ta jihar Kano da Kungiyoyin mata da matasa da na jam'iyyun siyasa da kungiyoyin lauyoyi mata." in ji Wayya.

A cewarsa, baya ga neman a kafa rundunar yan sanda a jihohin Najeriya, sun amince a goyi bayan a bai wa kananan hukumomi da bangaren shari'a da majalisa yancin gashin kai.

Abdullahi Wayya ya kara da cewa a taron, jama'a sun amince a sami karin jihohi a jihar Kano sannan kuma a samar wa masarautun gargajiya gurbi a kundin tsarin mulki domin ba su damar taka rawa kan batun tsaro.

"Sannan a ba su kariya da za ta hana yi wa masarautu katsalandan da kama karya." kamar yadda Wayya ya fada.

Shugaban kare Gamayyar ƙungiyoyin fararen hula a Kano ya ce daga cikin shawarwarin akwai neman a hade majalisar dokokin kasar a karkashin tuta daya.

Hakan a cewarsa zai taimaka wajen rage wa gwamnati nauyi - "majalisa guda daya ta isa duk abin da za ta yi." in ji Wayya.