Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 24Article 450933

BBC Hausa of Monday, 24 May 2021

Source: BBC

Sergio Aguero ya kusan komawa Barcelona

Sergio Aguero ya bar Manchester City shekaran ga Sergio Aguero ya bar Manchester City shekaran ga

Sergio Aguero ya kusan komawa Barcelona da zai buga wa tamauala a badi in ji kocin Manchester City, Pep Guardiola.

Aguero, mai shekara 32 zai bar Etihad idan yarjejeniyarsa ta kare a karshen kakar bana.

Dan wasan tawagar Argentina, ya ci wa Manchester City kwallo 260 a wasa 389 da ya buga mata.

''Watakila na bayyana sirri, kamar yadda Guradiola ya shaidawa BBC. Watakila ya kusan amincewa da kwantiragi a Barcelona.

''Zai je ya buga tamaula tsakanin fitattun 'yan wasan da suka shahara kamar Messi.''

Guardiola ya kara da cewar ''Ina da tabbacin zai ji dadin taka leda a kungiyar. Kuma watakila Barcelona za ta kara karfi a wasanninta tare da Aguero.''

Aguero ya buga wa City wasan karshe ranar Lahadi inda ya ci Everton kwallo biyu a karawar karshe a gasar Premier League ta bana.

Aguero ya koma Manchester City a kakar 2011 daga Atletico Madrid wadda ya yi wa wasa tsakanin 2006-11.

Ya koma taka leda a Spaniya daga Independiente wadda ya yi kaka uku da ita yana murza leda.