Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 24Article 450931

BBC Hausa of Monday, 24 May 2021

Source: BBC

Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Ronaldo, Bielsa, Konate, Kane, Zidane, Odegaard, Bissouma

Zinedine Zidane, shi zai ci gaba da horar Real Madrid? Zinedine Zidane, shi zai ci gaba da horar Real Madrid?

Manchester United tana saurare ta ji yadda za ta kaya a kan tsohon dan wasan gabanta Cristiano Ronaldo a Juventus, yayin da wakilin dan wasan na Portugal mai shekara , 36, ya ce lalle ba shakka tauraron zai iya barin kungiyar ta Italiya. (Jaridar Athletic)

Fatan Liverpool na sayen dan wasan tsakiya na Mali Yves Bissouma mai shekara 24 daga Brighton ya karfafa bayan da Arsenal ta yanke shawarar hakura da shi ta nemi wasu. (Jaridar Mail)

Sai dai kuma, shirin Liverpool din na cinikin dan bayan RB Leipzig dan Faransa, Ibrahima Konate, mai shekara 21, yana neman gamuwa da tangarda bayan da kungiyar ta Jamus ta nuna alamun cewa sai an biya cikakken kudin sakin dan wasan fam miliyan 34, da ke cikin yarjejeniyar barinsa kungiyar kafin ta sake shi - Saboda haka ne Liverpool din ke neman mayar da hankalinta kan Ozan Kabak dan Turkiyya wanda ke zaman aro mai shekara 21. (Jaridar Times)

Paris St-Germain na daga kungiyoyin da ake ganin za su yi nasarar daukar dan wasan tsakiya na Holland Georginio Wijnaldum, wanda zai bar Anfield saboda yarjejeniyarsa da Liverpool ta kare. Zuwa yanzu Barcelona ba ta mika bukatarta kan dan wasan mai shekara 30 ba. (Jaridar Le10Sport )

Kociyan Chelsea Thomas Tuchel yana son dan wasan gaba na Tottenham da Ingila Harry Kane, mai shekara 27, amma kuma Blues din na ganin abokan hamayyar tasu na yammacin Landan ba za su sayar musu da shi ba. (Jaridar Telegraph)

Shi kuwa tsohon dan wasan gaban Chelsea Tony Cascarino ya shawarci Tottenham da ta nemi dan wasan gaba na Aston Villa Ollie Watkins mai shekara 25, a matsayin wanda zai maye gurbin abokin wasansa na Ingila Harry Kane. (Talksport)

Kociyan Arsenal Mikel Arteta ya ce nan da 'yan makonni kungiyarsa za ta fara tattaunawa da Real Madrid a kan sabuwar yarjejeniya da dan wasanta na tsakiya da ke zaman aro Martin Odegaard, dan Norway mai shekara 22. (Jaridar Sun)

Rahotanni na nuna cewa Arsenal na son sayen dan wasan Roma Cengiz wanda ya yi zaman aro a Leicester City. AC Milan da Borussia Dortmund ma an ce suna son dan wasan gaban na gefe dan Turkiyya. (Tuttomercatoweb daga jaridar Mirror)

Leeds United ta yarda da sabuwar yarjejeniyar shekara daya da kociyanta dan Argentina Marcelo Bielsa, mai shekara 65, amma sai a cikin makon nan ne za a bayar da sanarwar a hukumance. (Jaridar Mirror)

Kociyan Norwich City Daniel Farke ya ce dole ne sai sun yi kasada fiye da sauran kungiyoyi a kasuwar 'yan wasa ta yanzu, idan dai har suna son ci gaba da zama a gasar Premier a kaka mai zuwa. (Jaridar Eastern Daily Press)

Barcelona na sha'awar dan wasan baya na bangaren hagu na Atalanta da Jamus Robin Gosens, mai shekara 26, wanda kuma aka ce Manchester City da Inter Milan da Juventus da AC Milan na sonsa. (Jaridar Sport ta Sifaniyanci)

Real Madrid za ta nemi sayar da dan wasanta na tsakiya dan Sifaniya Dani Ceballos a bazaran nan, sai dai Arsenal ba za ta nemi daukar dan wasan mai shekara 24 dindindin ba. (Jaridar 90min)

Bournemouth na son rike dan baya na Amurka Cameron Carter-Vickers, mai shekara 23, zaman dindindin bayan da ta aro shi daga Tottenham, amma kuma tana fuskantar gasa daga Newcastle United da Anderlecht. (SBI)

An nuna zabin kociyan Napoli Gennaro Gattuso a matsayin wanda ya fi dacewa ya karbi aikin horad da Juventus, wanda zai maye gurbin dan uwansa dan Italiya Andrea Pirlo, wand aba tabbas kan zamansa a kungiyar. (Tuttosport )

Haka shi ma kociyan Atalanta Gian Piero Gasperini, wanda kungiyarsa ta sha kasha a hannun Juventus a wasan karshe na kofin Italiya a makon da ya gabata, na cikin wadanda ake ganin aikin zai dace da su. (Calciomercato)

A kwanakin da ke tafe Zinedine Zidane zai tattauna da Real Madrid game da zamansa a kungiyar. (Jaridar ESPN)