Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 19Article 450857

BBC Hausa of Wednesday, 19 May 2021

Source: BBC

Kasuwar 'yan kwallo: Makomar Lewandowski, Kane, Lampard, Neto, Raul, Ginter

Robert Lewandowski, dan kwallon Bayern Munich Robert Lewandowski, dan kwallon Bayern Munich

Chelsea ta tuntubi Bayern Munich a kan cinikin dan wasanta na gaba Robert Lewandowski, dan Poland mai shekara 32, amma kuma kungiyar ta Premier za ta fuskanci gagarumar gogayya daga Paris St-Germain da Barcelona. (Daga Sky Sport)

Dan wasan gaba na Ingila Harry Kane na harin tafiyar da za ta kai ga sayensa sama da fam miliyan100 zuwa Manchester City a bazara, bayan da ya sheda wa Tottenham Hotspur yana son tafiya.

Manchester United na harin dan wasan mai shekara 27, amma kuma Chelsea ma da ke sonsa da wuya ta same shi domin Tottenham ba za ta so ta sayar wa abokan hamayyarta ba na London. (Jaridar Mirror)

Tuni Tottenham din ta fara shirya wa tafiyar Kane a watan Fabrairu, inda take duba yuwuwar dauko dan wasan da kungiyoyi da dama ke zawarci Erling Braut Haaland, dan Norway mai shekara 20, daga Borussia Dortmund. (Jaridar Mail)

Real Madrid ta tuntubi tsohon dan wasanta da kuma Sifaniya na gaba Raul, mai shekara 43, idan yana da sha'awar karbar aikin Zinedine Zidane na kociyanta. (Jaridar AS)

Sai dai kuma burin Real Madrid din na daukar gwanin dan wasan PSG da Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 22, zai iya gamuwa da cikas idan Zidane ya bar Bernabeu. (Eurosport)

Crystal Palace na tattaunawa da tsohon kociyan Chelsea kuma tsohon dan wasan tsakiya na Ingila Frank Lampard, mai shekara 42, domin maye gurbin Roy Hodgson. (Talksport)

Shi ma tsohon kociyan Bournemouth Eddie Howe, mai shekara 43, na daga cikin wadanda ake dubawa don gadar Hodgson, mai shekara 73 , yayin da kociyan Swansea Steve Cooper mai shekara 41, da kuma kociyan Barnsley, dan Faransa Valerien Ismael, mai shekara 45, su ma ke cikin 'yan takara. (Sky Sports)

Dan wasan Arsenal dan Brazil Willian mai shekara 32 na son tafiya kungiyar David Beckham, Inter Miami da ke Amurka. (Jaridar Sun)

Watakila Barcelona ta bar mai tsaron ragarta dan Brazil Neto ya tafi a bazara, inda Arsenal kuma ke son komawa zawarcin golan mai shekara 31. (Jaridar Mundo Deportivo)

Southampton na shirin taya dan wasan tsakiya na Borussia Dortmund, dan Denmark Thomas Delaney, mai shekara 29. (ESPN)

Tottenham ta mika bukatarta ta son sayen dan bayan Borussia Monchengladbach da Jamus Matthias Ginter, amma kuma tana fuskantar gogayya daga Liverpool da Inter Milan a kan dan wasan mai shekara 27. (Jaridar Bild)

Chelsea na son sayen dan wasan tsakiya na Atalanta, dan Ukraine Ruslan Malinovskyi, mai shekara 28, wanda Inter Milan da Paris St-Germain ma ke so. (Jaridar Sun)

Haka kuma Chelsean ta nuna sha'awarta ta sayen dan bayan Wolfsburg da Faransa Maxence Lacroix, mai shekara 21. (Sky Sports)

Arsenal ta taya dan wasan tsakiya na Norway Sander Berge fam miliyan 17 da dubu 200, amma kuma kungiyar dan wasan mai shekara 23, Sheffield United wadda za ta fadi daga Premier ta koma gasar Championship ta ce tana son fam miliyan 25 da dubu 800 ne akalla da kuma sharadin ba ta wani kaso a gaba idan Arsenal din za ta sayar da shi. (London.Football)

Newcastle United ta dauki zabin kara wa dan wasan baya na Wales Paul Dummett mai shekara 29, har wata 12 a kwantiraginsa. (Football Insider)

Dan bayan Manchester United Diogo Dalot, yana son barin kungiyar ya koma AC Milan zaman dindindin idan lokacinsa na aro a kungiyar ta ITaliya yak are a bazara. (Jaridar Calcio Mercato ta ruwaito daga Sun)

Liverpool ta kara tashi tsaye kan nuna bukatarta ta sayen dan wasan tsakiya na Portugal Pedro Goncalves, inda ta tuntubi Sporting Lisbon kan cinikin dan wasan mai shekara 22. (Record daga Team Talk)

An kawar da Arsenal daga zawarcin dan wasan tsakiya na Rennes Eduardo Camavinga, mai shekara 18, duk da yadda ake ta maganar tafiyar matashin dan wasan na tawagar Faransa ta 'yan kasa da shekara 21. (Jaridar Express)

Lazio ta yi nisa a kan tattaunawa da dan bayan Inter Milan dan Italiya Danilo D'Ambrosio, mai shekara 32, wanda kwantiraginsa da kungiyar ta Serie A zai kare a karshen kakar nan. (Jaridar Tuttomercato)