BBC Hausa of Sunday, 16 May 2021
Source: BBC
Citta wata nau'in saiwa ce da masana suka bayyana cewa ta samo asali ne daga yankin Kudancin Asia, kuma tana daga cikin kayan kamshi da ake amfani da su wajen dafe-dafen abinci ko kuma abin sha.
Ana kuma iya amfani da citta a danyar ta, ko busasshiya ko a garin ta har ma da ruwan ta, kuma tana da saukin samu a kasuwanni a fadin duniya.
A wasu lokutan akan hada ta da wasu sinadaran gyaran fatar jiki da kuma abinci.
Baya ga kasancewa daya daga cikin nau'ukan kayan kamshi da ake amfani da su wajen kara armashin girki, citta tana da dadadden tarihi na amfani a fannonin magungunan gargajiya da dama.
Masana harkokin abinci sun ce kamshi da dandano na musamman da citta ke da su na fitowa ne daga man da ake samu daga jikinta, kana mafi muhimmanci shi ne sinadarin 'gingerol' mai kunshe da sinadaran magani masu karfi.
Binciken masana
Masana kimiyya da suka gudanar da bincike mai zurfi a kan citta, da kuma kwararru a fannin hada magungunan gargajiya da sarrafa kayan kamshi, da saiwoyi da tsirrai, sun bayyana dimbin amfanin da citta ke da shi ga lafiyar jikin dan adam ta hanyoyi da dama.
Mujallar kiwon lafiya ta ''Healthline'' da ke Birtaniya ta wallafa binciken masana da ya gano wasu abubuwa game da citta da suka hada da magance ciwon gabobi, da rage kaifin kwayoyin halittar da ke haddasa cutar kansa a jikin dan adam da sauransu.
Masana daga Cibiyar Bincike ta Hormel a Jami'ar Jami'ar Minnesota ta Amurka sun gudanar da wani bincike mai zurfi game da citta a kan wasu beraye a shekarun baya, inda sakamakonsa ya nuna cewa sinadaran da ke jikin citta suna saurin kashe kwayoyin halittar cutar kansa.
Kazalika wani bincike na biyu da Kungiyar Masu Bincike kan Cutar Kansa ta Amurka ta gudanar ya nuna cewa cittar na rage kaifin yaduwar kwayoyin halittar kansar mafitsara.
Kuma akan yi amfani da ita wajen magance tashin zuciya, mura da kakamantansu kamar yadda binciken masana kimiyya ya nuna.
Nicola Shubrook, wata kwararriya a fannin abinci mai gina jiki da kula da lafiyar al'umma da ke Birtaniya wacce ta gudanar da bincike kan amfanin shayin citta, ta yi wa BBC karin bayani cewa citta tana da matukar amfani a jikin dan adam fiye da yadda ake tsammani.
Ta ce: "Citta tana taimakawa sosai wajen saukaka cutar hawan jini da kuma magance tashin zuciya da amai, musamman ida aka yi shayi da iya."
Malam Hambali Musa, wani dattijo ne mai shekaru 78 a Najeriya da yake yawan amfani da citta, ya shaida wa BBC cewa al'ummomi daban-daban a fadin duniya sun dade suna amfani da citta don maganin ciwon gabobi, ciwon jiki kuma har yanzu hakan bai sauya ba.
"Don saboda citta aba ce da muka dade da yin imanin cewa tana da wasu sinadarai da ke hana ciwon jiki bayan gudanar da aikin karfi, da sauran cututtuka kamar su mura," in ji Hambali.
A tattaunawarsa da BBC, Malama Bilkisu Lawal Zarabid, wata kwararriya a fannin sarrafa kayan kamshi, da itatuwa da ganyaye da sauran tsirrai, ta bayyana cewa citta na matukar taimakawa a fannoni da dama na lafiyar dan adam don haka yake da matukar muhimanci a rika amfani da ita.
Ta kuma ce ana sarrafa citta a danyarta, ko busasshiya ko garin ta, har ma da man ta, kuma mata masu fama da amai da tashin zuciya lokacin da suke laulayin ciki kan yi amfani da citta don dakatar da amai.
"Har ila yau mata masu fama da ciwon mara kan yi amfani da citta wajen magani, kana ana sarrafa ta da wasu saiwoyi wajen hada maganin ciwon suga, da mura da ciwon kasusuwa wato ''Athritis'', ana kuma amfani da ita wajen sarrafa maganin haihuwa a gargajiyance," in ji Zarabid.
Ita ma Dr Katherine Marengo, wata kwararriya a fannin kiwon lafiya da abinci mai gina jiki, ta bayyana wa mujallar Healthline cewa wani bincike da aka gudanar kan mata masu juna biyu 120 ya nuna cewa wadanda suka sha giram 750 na garin citta a kullum cikin kwanaki 4 sun shaida samun saukin tashin zuciya da amai, ba kamar matan da ba su sha ba.
Maganin gyambon ciki
Sai dai malama Bilkisu Lawal ta ce shan citta ga masu gyambon ciki da aka fi sani da 'ulcer' kan haifar musu da matsala sosai saboda zafin da take da shi, don haka ko ga wadanda ba su da irin wannan matsala bai kamata su rika amfani da ita fiye da kima ba.
"A ka'ida shan citta in dai sau daya za ka sha, bai wuce ka sha kamar yatsa daya ba, idan kuma za ka sarrafa ne zuwa abin sha da ake kira "ginger shot" bai wuce ka markada kamar yatsa biyar ba a yi lemon tsami saboda yana wanke ciki," in ji ta.
A cewarta: "Tana cikin sinadarai ta farko wajen kokarin rage kiba, saboda yana wanke ciki da sauran dattin ciki idan ka juri sha da lemon tsami zai taimaka matuka wajen rage kitse na jiki da tumbi.''
Ga jerin abubuwan amfanin da citta ke yi ga jikin dan adam
An samo bayanai game da amfanin citta a jikin dan adam daga kwararru a fannin sarrafa itatuwa ta tsairrai na gargajiya da kuma mujallun kiwon lafiya da suka wallafa binciken masana kimiyya a kai kamar haka: