Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 12Article 450753

BBC Hausa of Wednesday, 12 May 2021

Source: BBC

Bob Marley: Shekara 40 bayan rasuwar shahararren mawakin rege

Bob Marley ya mutu ne ranar 11 ga watan Mayu na 1981. Bob Marley ya mutu ne ranar 11 ga watan Mayu na 1981.

Yau shekara 40 ke nan tun bayan rasuwar fitaccen mawakin nan na rege Bob Marley sakamakon cutar daji wato kansa a Miami, yana da shekara 36.

Ya mutu ne ranar 11 ga watan Mayu na 1981.

Mawakin yana daya daga cikin mawakan da suka fi shahara kuma ake matukar kaunarsa a fagen waka a tarihi, inda ya rera fitattun wakokin da suka hada da No Woman No Cry, One Love, da kuma Redemption Song.

Wakar Buffalo Soldier ita ce wakarsa da ta fi shahara a Birtaniya, inda ta zama ta hudu a watan Mayun 1983.

Mujallar Time ta ayyana kundin wakar da ya fitar a 1977 mai suna Exodus a matsayin Kundin Karni.

An haifi Marley a shekarar 1945 kuma mahaifinsa farar fata ne yayin da mahaifiyarsa bakar fata ce 'yar kasar Jamaica.

Ya shafe rayuwar yarintarsa a cikin talauci kuma bai faye ganin mahaifinsa ba, wanda sojan ruwa ne da ya yi aiki da gwamnatin Birtaniya.

Ya bar gidansu yana da shekaru 14 domin yin sana'ar waka a Kingston.

A shekarar 1972, Marley ya isa Birtaniya tare da tawagarsa mai suna The Wailers inda suka rika zaga kasar tare da Johnny Nash yana fatan kaddamar da sana'ar wakarsa ga duniya.

Shekara guda bayan haka, The Wailers suka fitar da kundin wakoki mai suna Catch a Fire sannan suka fito a hirar talbijin a BBC.

Hirar da suka yi ta yi gagarumin tasiri inda suka samu masoya a kasashe daban-daban.

A wani balaguron waka da ya yi a 1975, sun rera wakar No Woman No Cry kai-tsaye a The Lyceum, London, inda aka saki wakar lamarin da ya bai wa Marley shahararsa ta farko a Birtaniya.

Daga nan mawakin ya shiga waka gadan-gadan inda aka san shi a ko ina a fadin duniya.

An san Marley a matsayin mai bin addinin Rastafaria, shi da matarsa Rita, inda suke sanya addinin nasu a cikin wakokinsa.

Mawakin yana matukar son kwallon kafa kuma yakan murza leda kafin ya rera waka ko kuma bayan ya gama.

"Ina son waka da kwallon kafa," a cewarsa a wata hira da ya yi a 1980.

Marley ya rera wakarsa ta karshe kai-tsaye a Birtaniya ranar 13 ga watan Yulin 1980 a New Bingley Hall, Stafford.

Marley ya mutu shekara daya bayan haka sakamakon cutar kansa, wadda aka gano yana dauke da ita a 1977. An binne shi a kauyensu Nine Mile da ke kasar Jamaica.