Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 10Article 450703

BBC Hausa of Monday, 10 May 2021

Source: BBC

Kasuwar 'yan kwallo: Sulemana, Rice, Kane, Bellingham, De Ligt, Taylor-Hart, Szczesny

Kociyan Arsenal Mikel Arteta Kociyan Arsenal Mikel Arteta

Kociyan Arsenal Mikel Arteta ya yi kira ga hukumar kungiyar da ta ware makudan kudade ta sayi 'yan wasa domin tabbatar da ganin kungiyar ta ci gaba da zama cikin masu gogayyar cin kofin gasar Premier. (Jaridar Star)

Haka kuma Arsneal din na son kulla sabuwar yarjejeniya da gwanin matashin dan wasanta na gefe Kido Taylor-Hart, dan Ingila mai shekara 18 a wata mai zuwa. (Jaridar Sun)

Ajax na shirin gogayya da Manchester United wajen sayen dan wasan gefe na kungiyar FC Nordsjaelland ta Denmark, dan kasar Ghana mai shekara 19. (Jaridar Mail)

Dan wasan tsakiya na West Ham Declan Rice ya nuna cewa yana son barin kungiyar domin tafiya wata kungiyar ta Turai. Daman Manchester United da Chelsea sun jima suna sha'awar dan wasan dan Ingila mai shekara 22. (Jaridar Mirror)

Dan wasan gaba na Tottenham Harry Kane na gaba-gaba a 'yan wasan da Chelsea, ke sha'awar saye. Kungiyar na shirin kashe kudi sosai wajen sayen dan wasan na Ingila mai shekara 27, idan dai har Tottenham za ta sayar da shi. (Jaridar Football Insider)

Manchester United ta zaku a sayar mata dan wasan tsakiya, dan Ingila Jude Bellingham, mai shekara 17, daga Borussia Dortmund a bazaran nan, maimakon abokin wasansa a kungiyar ta Jamus Jadon Sancho, mai shekara 21. (Jaridar Bild, daga Manchester Evening News)

Sai dai kuma Bellingham din yana son ci gaba da zama a Dortmund, wadda abu ne mai wuya ta yarda ta sayar da matashin dan wasan, bayan da ta kasa United wajen sayensa kasa da wata 12 da ya wuce. (Daga shafin Twitter na wakilin Sport 1 Patrick Berger)

Juventus ba ta da niyyar sayar da dan wasan bayanta na tawagar Holland Matthijs de Ligt, wadda daman tuni ta yi watsi da bukatar Chelsea da Barcelona ta sayen dan wasan mai shekara 21. (Jaridar Tuttosport )

Newcastle United ta tsawaita yarjejeniyar zaman dan wasanta na baya dan Switzerland Fabian Schar, inda yanzu dan wasan mai shekara 29 zai ci gaba da zama har shekara ta 2022 (Blick ta shirin kai tsaye na Chronicle)

Everton na son sayen tsohon mai tsaron ragar Arsenal, dan Poland Wojciech Szczesny daga Juventus a bazaran nan, amma kuma Paris St-Germain ma na sha'awar golan mai shekara 31. (Jaridar Calciomercato)

Dan wasan tsakiya na Sheffield United, dan kasar Norway Sander Berge, wanda ake dangantawa da tafiya Arsenal da Aston Villa da kuma Everton, mai yuwuwa ya bar kungiyar a kan fam miliyan 35, saboda sharadin faduwa daga gasar Premier na ka'idar yarjejeniyar zamansa a kungiyar. (Yorkshire Live)

West Ham na son sake sayo dan wasan gabanta na da Marko Arnautovic daga Shanghai SIPG, ta China, yayin da Crystal Palace da Everton da Inter Milan da kuma AC Milan dukkansu aka ce suna sha'awar dan Australian mai shekara 32. (Il Resto del Carlino, daga jaridar Sunday Mail)

Chelsea na son kulla doguwar yarjejeniya da dan wasan gabanta mai shekara 19 Armando Broja saboda yadda matashin dan wasan na kasar Albania ya taka rawar-gani a zaman aro na shekara daya da ya yi a kungiyar Vitesse Arnhem, inda ya ci kwallo 10. (Jaridar Sun ta Lahadi Sunday)

Sabon kociyan Roma Jose Mourinho na son dauko dan wasan gaba na Italiya Andrea Belotti mai shekara 27 daga Torino, tare kuma da dan wasan gaba na Argentina Mauro Icardi na Paris St-Germain.

Sannan ana ganin kila kungiyar ta Roma ta ci gaba da rike Edin Dzeko mai shekara 35, wanda da ake ganin za ta rabu da dan wasan na kasar Bosnia a bazaran nan. (Jaridar Corriere dello Sport)

Har yanzu Barcelona na sha'awar matashin dan wasan tsakiya na Ajax Ryan Gravenberch, mai shekara 18, wanda tun yana dan shekara 15 ta so sayen dan kwallon na Holland. Sai dai kuma kungiyoyi da dama da suka hada da Manchester United da Juventus na sonsa suma. (Jaridar Mundo Deportivo)

Shugaban Bayern Munich Herbert Hainer y ace kungiyar ta Jamus ba za ta kashe wasu kudade masu yawa ba wajen sayen 'yan wasa a bazaran nan, abin da ke nun aba za ta sayi dan wasan gefe na Moroko Achraf Hakimi ba mai shekara 22 daga Inter Milan ba. (Jaridar Goal)

Kociyan Liverpool Jurgen Klopp ya tabbatar wad an wasan tawagar Japan na tsakiya Takumi Minamino, mai shekara 26, wanda ke zaman aro a Southampton, cewa yana daga cikin tsare-tsaren kungiyar na gaba. (Jaridar Goal)