Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 02Article 450545

BBC Hausa of Sunday, 2 May 2021

Source: BBC

Kungiyar al Qaeda ta ce ta yi nasara da ficewar sojin waje a Afghanistan

Amrka za ta kammala ficewar sojojin ne zuwa ranar 11 ga watan Satumba Amrka za ta kammala ficewar sojojin ne zuwa ranar 11 ga watan Satumba

Yayin da kwamandan rundunar sojojin waje da Amurka ke jagoranta a Afghanistan Janar Scott Miller ya yi gargadi a kan kai wa dakarunsu hari, yana mai cewa za su mayar da martani da karfi idan aka taba su, kungiyar al-Qaeda na nuna cewa ficewar dakarun nasara ce a wurinta.

Janar Miller ya yi gargadin ne bayan da sojojin suka fara ficewa daga Afghanistan bayan zaman kusan shekara ashirin, yana mai cewa suna da damar da za su iya mayar da martini da karfi.

Za a kammala ficewar sojojin ne zuwa ranar 11 ga watan Satumba, sama da wata hudu ke nan da Amurka ta kulla yarjejeniya da Taliban a shekarar da ta wuce.

Saba ainahin lokacin ficewar ya sa Taliban ta yi barazanar komawa kai musu hare-hare.

Janar Miller ya ce komawa tashin hankali da rikici abu ne da zai kasance rashin kan gado wanda kuma ba zai zamo alheri ba, illa ya haifar da takaici kawai.

Amma kuma ya nuna karara cewa dakarun da ke ficewa daga kasar ta Afghanistan suna da kayan aiki da za su iya kare kansu.

Kwamandan na Amurka ya yi kalaman ne jim kadan bayan da kakakin Taliban ya fitar da sanarwa mai gargadin cewa, saboda Amurka ta karya yarjejeniyar da suka kulla a shekarar da ta gabata ta kammala janye sojojin zuwa ranar daya ga watan Mayu,

jinkirin da ya harzuka Taliban din, kungiyar ta ce babu wani hakki da ya rataya a wuyanta na mutunta yarjejeniyar, na kin kai wa sojojin waje hari.

Tun kan aje ko'ina rahotanni sun ce mayakan Taliban sun kai hari gundumar Ghazni, a dai dai wani shingen binciken jami'an tsaro.

Wata 'yar majalisar dokokin Afghanistan din kuma 'yar hadakar da ke mulkin kasar, Mariam Solaiman-khail, ta gaya wa BBC cewa tana fargabar abin da zai samu kasar bayan ficewar sojojin Amurka.

Ta ce: ''Abin tayar da hankali ne , saboda babu wata tattaunawa a kan wasu sharudda kan ficewar dangane da 'yancin mata da 'yancin yara, da 'yancin marassa rinjaye a wurin 'yan Taliban.

Abin fargaba na duniya shi ne cewa a jiya al Qaeda ta bayyana cewa, hakan wata nasara ce a gare ta. Wannan ya ba wa kungiyoyin 'yan ta'adda karin kwarin guiwa na su ci gaba da fada.

Abin tsoro ne matuka ganin yadda suke samun kwarin guiwa.''

'Yar majalisar ta Afghanistan ta kuma ce an samu gagarumin ci-gaba a fannin dumokuradiyya tun zuwan Amurka kasar.

Dukkanin wannan dai na zuwa ne bayan watanni na rashin tabbas, karuwar hare-haren 'yan bindiga, da kuma rugujewar shirin zaman lafiya na kasar, wanda da dama 'yan kasar ke da fatan zai kare su daga sake fadawa yakin basasa.