Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 04 28Article 450467

BBC Hausa of Wednesday, 28 April 2021

Source: BBC

Boko Haram: Dalilai biyar da suka sanya kungiyar ta zafafa kai hare-hare a Nigeria

Mayakan kungiyar Boko Haram na cikin kai hare-hare a arewa maso gabashin Najeriya Mayakan kungiyar Boko Haram na cikin kai hare-hare a arewa maso gabashin Najeriya

Mayakan kungiyar Boko Haram da ke da sansani a arewa maso gabashin Najeriya sun zafafa kai hare-hare a wasu jihohin yankin a baya-bayan nan.

Rahotanni sun nuna cewa tun a farkon watan Ramadan ne 'yan kungiyar ta Boko Haram suka soma bazuwa zuwa sassa daban-daban a yankin.

Sai dai bayanai sun nuna cewa mayakan kungiyar sun soma tayar da hankula ne lokacin da suka shiga garin Geidam da ke jihar Yobe ranar Juma'a inda suka cinna wa wasu wurare wuta sannan suka kashe mutane da dama.

Wasu mazauna garin da suka yi magana da BBC Hausa sun shaida mana cewa 'yan kungiyar ta Boko Haram sun yi ta musayar wuta da sojojin Najeriya a bayan garin.

Kazalika sun kashe mutane da dama ciki har da wata mata mai shayarwa, kamar yadda 'yar uwarta da a yanzu take rike da jaririyar da ta bari ta shaida wa BBC.

Sai dai rundunar sojin kasa ta Najeriya ta ce tana fuskantar matsala wajen fitar da mayakan kungiyar ta Boko Haram daga garin na Geidam saboda sun riga sun saje cikin jama'a.

Mai magana da yawun rundunar Mohammed Yerima ya shaida mana cewa sun kashe mayakan kungiyar ta Boko Haram 21 sanadiyyar ba-ta-kashin da suka yi da su.

Baya ga garin na Geidam, mayakan Boko Haram sun kai hari kan sansanin sojin Najeriya da ke garin Mainok na jihar Borno inda rundunar soji ta tabbatar da cewa sun kashe sojoji bakwai da kwamandansu guda daya.

Sai dai rahotanni sun ce, mayakan na Boko Haram, wadanda ke cikin manyan motocin yaki lokacin da suka kai harin, sun kashe fiye da sojoji 30.

Bugu da kari gwamnan jihar Neja da ke arewa ta tsakiyar Najeriya ya ce 'yan kungiyar ta Boko Haram sun mamaye wasu kauyuka na jihar inda suka kafa tutocinsu yana mai cewa suna dab da Abuja babban birnin kasar.

Abin da ya sa suke matsa kaimi.

Masana harkokin tsaro sun soma yin tsokaci game da dalilan da suka sanya mayakan na boko Haram suke zafafa kai hare-hare a 'yan kwanakin nan.

Barista Audu Bulama Bukarti, wani masanin tsaro da ke bincike kan ta'addanci a Cibiyar Tony Blair ta Birtaniya, ya shaida wa BBC cewa da ma can ba a ci karfin 'yan kungiyar ta Boko Haram ba.

"Na farko ya kamata mu gane cewa da ma wannan matsalar ba magance ta aka yi ba. Kamar yadda muka yi ta fada a baya, 'yan kungiyar da ma suna nan sun yi likimo ne a dazukansu suna tare da makamansu kuma suna ci gaba da kara kwarewa ne da kuma kara gina makamansu domin su kawo wadannan hare-hare,' in ji Barista Bukarti.

Ya lissafa karin dalilan da suka sanya mayakan na Boko Haram suka matsa kai hare-hare a baya bayan nan:

Neman karin lada a watan Ramadan

Masanin ya ce zuwan watan Ramadana ya sanya mayakan kungiyar Boko Haram sun matsa kai hare-hare saboda a ganinsu hakan zai sa su samu karin lada daga wurin Allah.

"A akidar mutanen nan sun yi imani cewa aikin da suke yi jihadi ne kuma lada za su samu a wurin Ubangiji game da abin da suke yi na kisan al'umma. Kuma wannan akida tasu na koyar da su cewa kasancewar watan Ramadan wata ne na neman gafara da gwaggwaban lada, to babu ladan da ya fi su yi irin wannan abin da suke kira jihadi a cikin watan Ramadana, in ji Barista Bukarti.

Sakwarkwacewar sojojin hadin-gwiwa

Masanin ya kara da cewa wani abu da ya sa 'yan Boko Haram suka matsa kai hare-hare a baya bayan nan shi ne sakwarkwacewar aikin hadin gwiwa da ake yi tsakanin sojojin Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi wadanda ake kira Muti-national joint taskforce.

A cewarsa, tun daga shekarar da ta gabata hadin kai tsakanin kasashen yake fuskantar barazana lamarin da ya sa tsohon shugaban kasar Chadi Idriss Deby ya rika bayyana cewa kasashe irin su Najeriya ba sa bayar da gudunmawar da ta kamata a yaki da kungiyar Boko Haram.

Ya kara da cewa hakan ya bai wa 'yan Boko Haram damar numfasawa da kara karfi saboda Chadi, wadda ita ce ta fi yaki da su, ta janye sojojinta da dama daga yankin Tafkin Chadi.

Jibge sojoji a manyan sansanoni

Barista Bulama Bukarti ya ce matakin da rundunar sojin Najeriya ta dauka na jigbe sojoji a manya-manyan sansanoni, wanda a turance ake kira super camp, ya taka muhimmiyar rawa wajen kara wa mayakan Boko Haram karfi.

An dauki matakin ne a 2019 lamarin da ya sa aka janye sojojin daga garuruwa irin su Geidam da Goza da kuma hanyoyi.

"Wannan ne ya ba [ Boko Haram] dama su yi yawo yadda suka ga dama sanna su tattara makamai da sauran kayan aiki da suke bukata ta hanyar tare mutane suna yi musu kwace sannan ya ba su dama su kai hare-hare duk inda suka ga dama," in ji Bukarti.

Ya ce kafa wadannan manyan sansanoni babban hadari ne domin kuwa mayakan na Boko Haram sun san inda sojoji suke a tattare don haka za su iya kai musu hari kamar yadda suka yi a Mainok.

Rashin kayan aiki

Mai binciken kan lamarin tsaro ya ce koke-koken da sojoji suka kwashe tsawon lokaci suna yi kan rashin isassun kayan aiki na cikin abubuwan da suka karfafa gwiwar Boko Haram ta tsananta kai hare-hare.

A cewarsa: "Wadansu sojojin sun shekara biyar zuwa shida suna yaki a borno da Yobe da sauran bangarori an ki canza su wanda a tsarin aikinsu kamata ya yi a canza su cikin shekaru biyu a kawo wadansu sabbi domin su ma su je su huta su gana da iyalinsu.

To, an bar su a nan sun gaji da wannan yaki. Sannan kuma ba su da isassun makamai; wadansunsu suna kuka cewa hatta takalman da za su saka su suke saya da kudinsu."

Rabuwar kungiyar Boko Haram

Barista Audu Bulama Bukarti ya ce rabuwar da kungiyar Boko Haram ta yi inda wasu suka balle suka kafa nasu bangaren ta ta'azzara hare-haren da mayakan kungiyar suke kai wa jama'a.

Ya ce kodayake wasu suna ganin rabuwar a matsayin wata hanya ta wargajewar kungiyar amma a zahiri hakan ya sa suna yin gasa wajen kai hare-hare.

"Idan muka duba kungiyoyi a fadin duniya baki daya. Misali, Al-Qaeda wadda daga baya suka rabu aka samu kungiyar ISIS, za ka ga cewa idan aka samu irin wannan rabuwa ba lallai ne ya zama alheri ga kasa ba.

Domin suna fara gasa ne a tsakaninsu, idan suna gasa kuma za su yi wa zai fi yawan makamai da kwarewa da yawan kai hare-hare kuma haka suke yi a yanzu a arewa maso gabas: Shekau yana so a ce shi ne shugaban 'yan ta'adda, su ma ISWAP suna so a ce su ne shugabannin 'yan ta'adda. Saboda haka wannan gasar da suke kara musu kwarewa da kayan aiki take yi, sannan kasancewarsu a bangarori daban-daban ya raba wa sojoji hankali."