Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 04 24Article 450409

BBC Hausa of Saturday, 24 April 2021

Source: BBC

Dubban mutane ne suka halarci jana'izar Idris Deby

Anyi jana'izar Idriss Deby ranar Jum'ah Avrilu 23 a N'Djamena Anyi jana'izar Idriss Deby ranar Jum'ah Avrilu 23 a N'Djamena

Dubban 'yan kasar Chadi ne suka halarci jana'izar ban girma da aka yi wa daɗaɗɗen shugaban kasar Idriss Déby wanda 'yan tawaye suka kashe a farkon wannan makon.

Cikin shugabannin kasashen da suka halarci jana'izar har da shugaban Faransa Emmanuel Macron, wanda babban aminin kasar Chadi ne a yaƙi da 'yan ta'adda da ke yankin.

Ya tsaya kan akwatin gawar marigayin inda ya gabatar da jawabi da cewa; "ka rayu a matsayin soja, ka mutu a matsayin soja dauke da makami a hannunka.

"Ka sadaukar da rayuwarka ga kasar Chadi domin kare al'ummarka."

Ya shaida wa mahalarta jana'izar a filin wasa na la Place la Nation da ke birnin N'Djamena cewa: "Ba za mu yadda da wata barazana da Chadi za ta fuskanta a yau ko gobe ba ko janyo rashin tabbas kan zaman lafiya da martabar kasar."

Sojoji sun yi faretn ban girma ga marigayin, dan sa Janar Mahamat Kaka Beby Itno, wanda sojoji suka sanar zai jagoranci kasar ya gabatar da jawabi a wajen.

Ya sha alwashin zai yi koyi da mahaifinsa, da ci gaba abin da mahaifinsa ya yi fice a kai wato, sasantawa, zaman lafiya, yafiya da hada kan al'ummar kasar Chadi.

A ranar Talata ne sojoji suka sanar ce wa s Shugaba Idris Deby ya mutu ne a fagen daga, domin yakar 'yan tawayen FACT da ke arewacin kasar.

Baya ga shugaban Faransa a wajen jana'izar, su ma shugabannin kasashen Guinea, da Mali, da Mauritania da jamhuriyar Nijar da Najeriya, sun yi watsi da gargadin da 'yan tawayen suka yi na kar su halarci jana'izar saboda dalilai na tsaro.

Bayan kammala jawaban da sojoji suka yi na ban girma ga marigayi Deby, an yi masa salla a babban Masallacin Juma'a da ke N'Djamena.

Daga nan jirgin sama ya dauki gawar zuwa kauyen Amdjarass, da ke kusa da mahaifar marigayin a garin Berdoba, sama da kilomita 1,000 daga babban birnin kasar, kuma kusa da iyakar Chadi da Sudan.

Labarin rasuwarsa a ranar Talata ta girgiza shugabannin kasashe daban-daban, inda suka fara tura sakon ta'aziyya da yabo ga marigayin.

Shugaba Macron ya kira shi da ''babban aboki''. Shugaba Paul Biya na Kamaru ya ce ''ya yi aiki tukuru ba tare da gajiyawa ba.''

Shugaba Felix Tshisikedi na Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo ya ce ''Mutuwar Deby babbar asara ce ga Chadi da nahiyar Afirka.''

Shi kuwa Bah Ndaw na Mali cewa ya yi ''mutuwar ta girgiza shi matuka.'' Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka Ta Kudu ya ce ''an yi wa jarumi kisan gilla.''

Shugaba Deby shi ne ja gaba a yaki da 'yan ta'adda da ta'addanci a yankin Sahel, Chadi ta yi suna wajen kyankyashe zaratan sojoji da kayan yaki a Afirka Ta Yamma, sojojin kasar ke yaki da 'yan tawaye masu alaka da kungiyar al-Qaeda da IS.

Sojojin kasar karkashin jagorancin dan marigayin Janar Mahamat Kaka sun karbi iko da kasar bayan mutuwarsa.

Jam'iyyun adawa dai sun yi watsi da zabar dan marigayin a matsayin shugaban kasa. su ma 'yan twayen sun yi watsi da zabin sojojin, amma sun kira dakatar da bude wutar wucin gadi a ranar juma'a da ake yin jana'azar.

A wata sanarwa da suka fitar, 'yan tawayen sun ce an sanya bam a cibiyoyinsu guda biyu a safiyar Juma'a, sai dai ba yi karin bayani a waje da wadanda lamarin ya rutsa da su ba ko asarar rai.