Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 03 18Article 449733

BBC Hausa of Thursday, 18 March 2021

Source: BBC

Kano Pillars ta ci Kwara United a gasar Firimiya

Sun yi karo ne a wasan mako na 16 a gasar Firimiyar Najeriya Sun yi karo ne a wasan mako na 16 a gasar Firimiyar Najeriya

Kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta yi nasara a kan Kwara United da ci 2-0 a wasan mako na 16 a gasar Firimiyar Najeriya ranar Laraba.

Pillars ta ci kwallo ta hannun kyaftin Rabiu Ali a bugun daga kai sai mai tsaron raga, sannan Usman Babalolo ya ci na biyu daf da za a tashi daga karawar.

Da wannan sakamakon Pillars, wadda ta ci wasa takwas da canjaras uku a bana ta koma ta uku a kan teburi da maki 27.

Kwara United wadda ta sha kashi a hannun Pillars, itama maki 27 ne da ita tana kuma ta biyu a teburin.

Enugu Rangers mai kwantan wasa daya ita ce ta daya a teburin itama da maki 27.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga:

Heartland 2-0 Wikki Tourists

Warri Wolves 0-0 Jigawa Golden Stars

Rivers United 2-0 Mountain of Fire

Akwa United 1-0 FC Ifeanyi Ubah

Adamawa United 1-1 Abia Warriors