BBC Hausa of Thursday, 18 March 2021
Source: BBC
Wasu jiga-jigan jam`iyyar APC mai mulkin Najeriya sun fara yin kiran ya kamata jam`iyyar ta keɓe takarar shugabancin ƙasar a zaɓen 2023 ga yankin kudancin ƙasar.
Masu irin wannan ra`ayin na cewa yin hakan shine adalci ga kudancin ƙasar, tunda ɗan arewa, wato shugaba Muhammadu Buhari ne ya samu wa`adin mulki biyu a ƙarƙashin tutar jam`iyyar, don haka sake tsayar da ɗantakara daga yankin arewa zai zamanto tauye haƙƙin ƴan kudu.
Senata Mohammed Ali Ndume, ɗan majalisar dattawan ƙasar ne mai irin wannan ra`ayin, kuma ya shiadawa BBC cewa ya kamata ya kasance an gina jam'iyyar APC a kan adalci, irin wanda aka yi lokacin da aka nemi arewa ta bayar da ɗan takara.
A cewarsa, ''Haka aka yi har aka goyi bayan shugaba Muhamadu Buhari, mutum ɗaya ne daga kudu wato Rochas Okorocha ya fito daga kudu, kuma shima ya fito ne a ra'ayin kansa ba tare da goyon bayan jam'iyya ba, shi yasa ma bai samu nasara ba''.
Ya ƙara da cewa kamata ya yi idan an zo zaɓen 2023 a ramawa kura aniyarta, ma'ana a goyawa kudu baya domin ta bayar da nata ɗan takarar, ''Daga nan sai muga abin da Allah zai yi'' inji Sanata Ndume.