Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 18Article 450838

BBC Hausa of Tuesday, 18 May 2021

Source: BBC

Zanga-Zanga ta shafi rashin kwazon United — Solskjaer

Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer

Ole Gunnar Solskjaer ya ce zanga-zangar da magoya baya suka yi kan masu Manchester United ya shafi rashin kwazon 'yan wasa kwanan nan.

A makon jiya Leicester City ta doke United, sannan Liverpool ta caskara kungiyar a Old Trafford, wadda ta yi wasa daf da daf, sakamakon soke fafatawa da kungiyar Anfield tun farko.

Cikin kwana takwas United ta buga karawa hudu da ta hada da wasa na biyu da Roma a Italiya a Europa League ranar 6 ga watan Mayu, inda ta yi rashin nasara da ci 3-2 a Italia.

Ranar 9 ga watan Mayu ta je ta doke Aston Villa 3-1 a Premier, sannan ta sha kashi a gida da ci 2-1 a hannun Leicester ranar 11 ga watan Matu, kwana biyu tsakani Liverpool ta doke ta da ci 4-2 a Old Trafford.

Bayan da United ta tashi karawa da Leicester City, kungiyar ta rike 'yan wasanta inda aka tanadar musu da gadon kwana a Old Trafford, don tunkarar Liverpool cikin kuzari.

''Bana son yin korafi kan wannan batun, saboda mun yi rashin nasara a wasa biyu a jere, amma dai zanza-zanga ce ta shafi rashin kwazonmu'' kamar yadda Solskjaer ya fada.

Idan United ta yi nasara a kan Fulham a wasanta na gaba a Premier League za ta kasance ta biyu a bana kenan, kuma karo na biyu da za ta yi hakan tun bayan da Sir Alex Ferguson ya yi ritaya a 2013.

Hakan zai kuma bai wa Solskjaer damar ajiye manyan 'yan kwallonsa a fafatawa da Wolves a wasan karkare Premier ta bana, domin fuskantar Villareal a wasan karshe a Europa League na bana.

United za ta karbi bakuncin Fulham wadda ta fadi daga gasar bana, domin buga Premier ranar 18 ga watan Mayu, sannan ta ziyarci Wolves ranar 23 ga watan Mayu kwana uku tsakani ta fafata da Villareal.