Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 06 02Article 451112

BBC Hausa of Wednesday, 2 June 2021

Source: BBC

Zamfara: Abin da ya sa muka kama masu zanga-zanga kan taɓarɓarewar tsaro

Usman Alkali Baba ne sabon shugaban yan sandan Nijeriya Usman Alkali Baba ne sabon shugaban yan sandan Nijeriya

Ƴan sanda a jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya sun sanar da kama wasu daga cikin mutanen garin Kuryar Madaro na ƙaramar hukumar Kauran Namoda, sakamakon wata zanga-zanga da suka fara gudanarwa ranar Litinin da nufin jawo hankalin hukumomi ga matsalar taɓarɓarewar tsaro da suke ciki.

Rahotanni sun ce masu zanga-zangar sun tare babbar hanyar yankin, inda suka hana ababen hawa wucewa tare da cin alwashin ci gaba da zaman dirshen har sai yadda hali ya yi.

A cewar SP Muhammad Shehu, jami'in hulda da jama'a na rundunar ya ce mutanen da suke zanga-zangar na kawo tarnaki ga aikin samar da tsaro a jihar.

Ya bayyana cewa mutanen ɓatagari ne kuma "ba zaman lafiya suke so ba" a don haka ya sa jami'ansu suka buɗe hanyar da masu zanga-zangar suka toshe domin bai wa jama'a damar gudanar da harkokinsu.

"Cikin wadanda suka gudanar da mugun aikin, mun kama bindigogi ƙirar gida da suka rinka amfani da su wajen tsoratar da mutane kuma suna nan wajen ƴan sanda domin gudanar da bincike a kansu", kamar yadda SP Shehu ya bayyana.

Tun da farko wani mazaunin garin ya shaida wa BBC cewa dalilinsu na gudanar da zanga-zangar ba ya rasa nasaba da yadda hukumomi suka yi burus da korafe-korafensu game da halin da tsaro yake ciki.

"Mun samu matsala wajen kwana 21, tun yaushe ɓarayi sun dame mu a kauyukanmu, mun nemi a taimaka mana ba a taimaka mana ba". in ji mazaunin garin.

Ya ce za su ci gaba da gudanar da zanga-zangar har sai gwamnati ta yi wani abu a kai ko kuma ta taimaka musu.

Sai dai rundunar ƴan sandan ta bukaci duk wani mai korafi da ya gabatar da shi ta hanyar da ta gabata.

Kwanan baya ma, mutanen garin Ɗan sadau a jihar ta Zamfara sun yi wani yajin aikin zirga-zirgar ababen hawa tsawon kwanaki don nuna fushinsu kan ƙaruwar hare-haren 'yan fashin daji.