Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 06Article 450639

BBC Hausa of Thursday, 6 May 2021

Source: BBC

Zaftare albashi zai sa ma'aikata da dama cikin hali na kunci - NLC

Kungiyar kwadago ta Najeriya ta gargadi gwamnatin tarayya akan niyyan rage albashin ma'aikata Kungiyar kwadago ta Najeriya ta gargadi gwamnatin tarayya akan niyyan rage albashin ma'aikata

Kungiyar kwadago ta Najeriya ta gargadi gwamnatin tarayya da ta dakatar da yunkurin da take yi na rage albashin ma'aikata, tana mai cewa irin wannan mataki zai sa ma'aikata su shiga cikin wani hali na ha'u'la'i.

A ranar Talata ne minister kudi ta Najeriya Zainab Ahmed Shamsuna ta bayyana cewa gwamnati na nazari akan yadda za ta zaftare yawan kuɗaɗen da take kashewa ta hanyar rage albashin ma'aikata.

Rahotanni sun kuma ce ministar ta umarci hukumar albashin ma'aikata ta yi nazari akan albashi da yawan ma'aikatun gwamnati da ke kasar.

Sai dai shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya, Ayuba Wabba ya yi kira ga gwamnati a kan ka da ta zaftare albashin mafi kankanta na naira dubu talatin na ma'aikata, yana mai cewa albashin masu karbar albashi mai tsoka ne kawai ya kamata a rage musamman masu rike da mukaman siyasa.

"Abu ne da ba za a taɓa tsammani ba cewa gwamnati za ta yi niyya ta rage albashin ma'aikatan Najeriya a wannan lokacin''.

''Tambayar anan ita ce shin wani albashi ne gwamnati za ta zaftare? Ko shakka babu ba albashi mafi kankanta na naira dubu talatin ba ne wanda halin yanzu ba ya iya sayan buhun shinkafa.

Shugaban kungiyar kwadagon, yayin da yake bayyana matakin a matsayin "rashin tausayi" da "rashin tunani", ya ce ma'aikatan Najeriyar na bukatar a gaggauta janyewar matakin tare da neman afuwa daga Ministan Kudin kasar.