Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 18Article 450852

BBC Hausa of Tuesday, 18 May 2021

Source: BBC

Za a yi shekara goma kafin a gyara Gaza - Likita

Isra'ila ta ci gaba da yin ruwan bamabamai akan Gaza Isra'ila ta ci gaba da yin ruwan bamabamai akan Gaza

Taimakon magunguna da sauran kayayyakin asibiti da kasar Masar ta aika sun fara isa hannun jami'an lafiya na birnin Gaza inda alkaluma na baya bayan nan suka nuna cewa hare-haren sama da Isra'ila ke kai wa birnin a mako na biyu na rikici tsakaninta da 'yan gwagwarmayar Falasdinawa sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa sama da dari biyu da raunata sama da 1250.

Haka kuma motocin daukar marassa lafiya na Masar din na ta jigilar Falasdinawa da aka jikkata zuwa asibitoci a birnin Sinai da Alkahira.

Irin mawuyacin halin da aka shiga sakamakon munanan hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da kaiwa ta sama a birnin na Gaza da suka katse wutar lantarki da lalata tituna da haddasa karancin mai da sauran abubuwa na jin dadin jama'a, ga kuma wadanda ke mutuwa da jikkata daga hare-haren ya sa gwamnatin Masar ta shiga domin taimakawa.

Daman hukumar lafiya ta duniya, WHO, ta yi kira ga shugabannin Isra'ila da Falasdinawa da su kare ma'ikatan lafiya da asibitoci da sauran abubuwan jin dadin jama'a, inda ta kara da cewa rikicin ya yi matukar shafar aikin gwajin kwayar cutar korona da kuma na riga-kafinta.

Mohammad Abu Rayya, likitan yara ne a Gaza ya bayyana yanayin da ake ciki a asibitinsa:

Ya ce: "A kullum muna karbar wadanda hare-haren suka rutsa da su, masu bukatar kulawar gaggawa, muna karbar gawawwaki. Ba mu da dakin ajiye gawa babba, da zai iya daukar wadanda aka kashe da kuma gawawwaki. Halin da ake ciki a Gaza na ta tabarbarewa.''

Likitan Mohammad Abu Rayya, ya ce an lalata babban titin birnin na Gaza, wanda ta nan ne ake zuwa asibitocin birnin.

Ya ce mutanen da hare-haren ke tasa daga gidajensu daga yankin arewac na tururuwa zuwa cikin birnin Gaza, inda suke fakewa a makarantun Majalisar Dinkin Duniya, wanda hakan zai haddasa babbar annoba, da daman ana fama da annobar korona, mutane ne da ba su da komai, ba abinci, ba ruwa, ba su da ko katifa.

Ya ce ana bukatar akalla shekara goma a gyara abubuwan da Isra'ila ta lalata a Gaza.

Hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da Falasdinawa 'yan gudun hijira, wadda ke taimaka wa Falasdinawan a Gaza, da yankin gabar yamma da kogin Jordan da Jordan da Syria da Lebanon tsawon gomman shekaru ta ce halin da ake ciki ya zama tamkar na wanda ana kukan targade sai kuma ga karaya

Tamara Alrifai ita ce mai magana da yawun hukumar:

Ta ce: ''Gaza na ganin hare-hare na sama da tshin hankali mafiya tsanani wajen asarar rayuk da lalat kayayyakin jin dadin jama'a, da kuma kaduwar jama'a tun shekara ta 2014

Gaza ta kasance a kulle tsawon shekara 14, abin da ya raunana tattalin arzikinta gaba daya, kum hakan ya karya duk wani kwarin guiwa da burin matasa.

Rashin aikin yi ya yi tsanani, sannan kuma a shekarar da ta wuce sai ga annobar korona da ita ma ta shafi birnin na Gaza ainun, to gaba daya dai, lamarin ya jefa mawuyacin halin da daman ake ciki zuwa wani mataki na lahaula.''

Yanzu dai ba wutar lantarki a yawancin sassan birnin na Gaza , abin da ke shafar gudanar da ayyukan kula da jama'a. Israila ta kuma gaya wa Majalisar Dinkin Duniya cewa, akwai hadarin barin motocin dakon mai su shiga birnin.

Masar ta tura motocin mai amma zuwa lokaciun hada wannan rahoto ba su kai ga tsallaka wa iyakar Rafah ba.

A yunkurin dakatar da bude wuta kuma, wanda bai taka kara ya karya ba, shugaba Biden na Amurka ya gaya wa Firaminista Benjamin Netanyahu na Isra'ila cewa yana son ganin an dakata da rikicin a Gaza.

Biden ya yi maganar ne ta waya kwana daya bayan da Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya kasa cimma matsaya a kan sanarwar da zai fitar a kan rikicin, bayan da gwamnatin Amurkar ta Misa Biden ta hau kujerar-naki a kai.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya jaddada cewa za su ci gaba da ruwan bama-bamai a Gaza har sai abin da hali ya yi.