Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 03 02Article 449445

BBC Hausa of Tuesday, 2 March 2021

Source: BBC

Yankin Tigray: Sojoji sun kama wakilin BBC a Ethiopia

this is a test this is a test

Sojojin Ethiopia sun kama wakilin BBC a yankin arewacin Tigray mai fama da rikici.

Girmay Gebru, wakilin sashen BBC Tigrinya, an kama shi ne tare da wasu mutum huɗu a wani wurin shan gahawa a Mekelle babban birnin yankin.

Shaidu sun shaida wa BBC cewa sojoji ne sanye da kakin soja suka kama mutanen biyar suka tafi da su cikin ayarin motocin soja.

Ba a san inda ake tsare da su ba kawo yanzu. BBC ta samu rahotannin da ke cewa an tafi da wakilinta a wani sansanin soji a Mekelle.

Yankin Tigray ta kasance ƙarƙashin ikon sojoji tun watan Nuwamban bara, lokacin da Firaministan Habasha ya sanar da cewa dakarun ƙasar sun ƙwace ikon yankin bayan ƙaddamar da farmaki kan ƴan tawayen Tigray.

    Abin da rikici a yankin Tigray na Ethiopia yake nufi Rikicin Tigray: Dakarun Habasha sun kutsa cikin yankin
Rikicin ya ƙazance ne bayan da ƴan tawayen na TPLF suka ƙwace ikon wani sansanin soji a Tigray.

Ɗaruruwan mutane aka kashe tare da raba dubbai da gidajensu a rikicin, kuma ana bayyana damuwa kan rahotannin ta'addanci da munin ayyukan jin-ƙai.

A makon da ya gabata ne gwamnatin Ethiopia ta amince ƴan jarida na kasashen waje su bayar da rahoto kan rikicin Tigray bayan haramta wa ƴan jaridu shiga yankin tsawon wata ɗaya.