Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 03 23Article 449818

BBC Hausa of Tuesday, 23 March 2021

Source: BBC

'Yan sanda a Kano sun kama wanda ake zargin yana samawa 'yan bindigar zamfara babura

DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce sun kama mutumin da babura guda biyu DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce sun kama mutumin da babura guda biyu

Rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Kano ta ce ta cafke wani mutumi da take zargin yana samawa 'yan bindigar dake kai hare hare a jihar Zamfara baburan hawa.

Rundunar ta kama mutumin ne a jihar Kano, inda bayanai suka ce yana siyan babura domin tafiya da su jihar ta Zamfara, ya kuma sayarwa yan bindigar a kan farashi mai yawan gaske.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce yayin binciken da suka gudanar mutumin ya shaida musu cewa ya sayarwa da 'yan bindigar babura kusan 100, a kan kudi sama da Naira dubu dari shida duk ɗaya.

Ya ƙara da cewa mutumin kan baro Zamfara zuwa Kano ya sayi baburan sannan ya sake komawa can domin sayarwa yan bindigar, amma sai a yanzu aka kama shi, bayan samun bayanai daga wajen waɗanda yake sayan baburan a wajensu a jihar ta Kano.

"Babur yake sayarwa kirar Honda ACE 125, wanda ake kiransa da Boko Haram a can jihar Zamfara, wanda tuni gwamnatin jihar ta hana amfani da shi, in suka zo jihar Kano sai su saya su canja musu kwali, a haka suke shigar da shi daji, inda a can ake hada shi, sannan su yi amfani da shi wajen kaiwa mutane hare hare."

DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce sun kama mutumin da babura guda biyu, wadanda har an canja musu kwali za a fitar da su daga jihar Kano zuwa jihar ta Zamfara.

An jima ana zargin cewa maharan da suka addabi jihar Zamfara da maƙwabtanta na amfani da babura ne wajen yin jerin gwano, sannan sukai hari ga jama'a, kuma su sace wasu.

Mutanen gari sun sha bada shaidar cewa ana kai musu hare hare ne a kan babura, abinda ya sa mahukunta a jihar Zamfara suka ɗauki matakin hana amfani da wasu daga cikin irin wadannan babura don tabbatar da tsaro.