Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 03 11Article 449591

BBC Hausa of Thursday, 11 March 2021

Source: BBC

'Yan Barcelona da za su kara da PSG a Champions League

'Yan kwallon Barcelona cikin murna 'Yan kwallon Barcelona cikin murna

Paris St Germain za ta karbi bakuncin Barcelona a wasa na biyu a zagaye na biyu a Champions League da za su kara ranar Laraba.

A wasan farko da suka buga cikin Fabrairu PSG ce ta doke Barcelona da ci 4-1 a Nou Camp, inda Kylian Mbappe ya ci uku rigis a fafatawar.

Kyaftin Lionel Messi ne ya ci wa Barcelona kwallo a bugun daga kai sai mai tsaron raga, sai Moise Keane da ya zura kwallo a ragar Barcelona.

Wannan ne wasa na 13 da za su kece raini a tsakaninsu a gasar zakarun Turai, inda Barcelona ta ci karawa biyar, PSG ta yi nasara a hudu da canjaras uku.

Sai dai dan kwallon Brazil, Neymar ba zai fuskanci tsohuwar kungiyarsa Barcelona ba kamar yadda bai yi ba a wasan farko sakamakon jinya.

Tuni kocin Barcelona, Ronald Koeman ya bayyana 'yan wasa 22 da za su fuskanci PSG a Faransa.

'Yan kwallon sun hada da Ter Stegen da Dest da Sergio da Griezmann da Pjanic da Braithwaite da Messi da Dembele da Riqui Puig da kuma Neto.

Sauran sun hada da Lenglet da Pedri da Trincao da Jordi Alba da Matheus da De Jong da Umtiti da Junior da Inaki da Ilaix da Konrad da kuma Mingueza.

'Yan wasan Barcelona da ke jinya sun hada da Pique da Araujo da Coutinho da Sergi Roberto da kuma Ansu Fati.