Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 03 14Article 449632

BBC Hausa of Sunday, 14 March 2021

Source: BBC

Yadda tashin bam ya haifar da mummunar ɓarna a Afghanistan

An ce fashewar ta faru ne kusa da ofishin 'yan sanda An ce fashewar ta faru ne kusa da ofishin 'yan sanda

Jami'an Afghanistan sun ce akalla mutane uku sun mutu kuma kusan hamsin sun ji rauni lokacin da wani bam da ke cikin mota ya fashe a yammacin garin Herat.

An ce fashewar ta faru ne kusa da ofishin 'yan sanda. Lamarin ya haifar da mummunar barna, da ta hadar da lalata gine gine da kona dukiyoyin jama'a.

Hotunan da aka watsa a shafukan sada zumunta sun nuna gine-ginen da suka rushe, da kuma mutanen da ke neman wadanda abin ya shafa da wadanda suka tsira a cikin baraguzan ginin.

Ba a san wanda ya kai harin ba, amma tashin hankali na karuwa a kasar, yayin da tattaunawar sulhu da 'yan Taliban ta ci tura, kuma har yanzu mayakan kungiyar IS ke ci gaba da kai hare hare.

Barazanar ɓarkewar yaƙin basasa a ƙasar

Wanni babban jam'in diflomasiya daga ƙungiyar Tarayyar Turai da ke ziyara a Afghanistan ya sanar da cewa ''akwai haɗari mai girman gaske game da yiwuwar ɓarkewar yaƙin basasa a ƙasar ganin yadda tashe -tashen hankula ke ci gaba da ƙazanta.

Kwamishinan kiyaye zaman lafiya da yaƙi da tashin hankali na ƙungiyar Janez Lenarcic, ya ce da akwai gagarumar alama da ke nuna cewa, babu wata nasara kan hanyoyin da ake bi wajen samar da zaman lafiya da aka soma a watan Satumbar da ya gabata, hanyoyin da tuni ake gani suna da matsala.

Jam'in ya buƙaci yin dukkan ƙoƙarin da ya dace wajen ganin cewa tattaunawa tsakanin gwamnati da wakilan 'yan kungiyar Taliban ba ta sha ruwa ba.

Ya kuma yi kira ga 'yan Taliban da ke kai hare-hare, da su kara yin kokari fiye da wanda suka yi a baya, wajen ganin wannan tattaunawa ta gudana.

Mista Lenarcic ya furta cewa, kusan rabin al'ummar kasar Afghanistan na ƙishirwar ganin an kawo karshen wannan tashin hankali da ke gudana, wanda kuma a halin da ake ciki ke haddasa mumunan yanayi ta bangaren aikin jin kai.