Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 27Article 450987

BBC Hausa of Thursday, 27 May 2021

Source: BBC

Yadda rage darajar Naira zai shafi rayuwar talaka a Najeriya

Baban bankin Najeriya kan rage darajar Naira lokaci zuwa lokaci Baban bankin Najeriya kan rage darajar Naira lokaci zuwa lokaci

Babban bankin Najeriya ya karya darajar Naira da kashi 7.6 cikin 100 kan dalar Amurka a dai-dai lokacin da ƙasar ke shirin amfani da dalar Amurka kawai wajen auna kadarin kuɗinta.

Babban bankin ya karya darajar daga Naira 370 ga dala 1 da ake amfani da shi a hukumance a sabon tsarin canji na Nigerian Autonomous Foreign Exchange (NAFEX), wanda a yanzu ya kai naira 410.25 ga dala 1 a cewar bankin.

Bankin ya bayyana sauyin a shafinsa kuma gwamnan bankin Godwin Emefiele ya bayyana cewa "mun gano cewa an daina sauya Naira da farashin da CBN a hukunmance, don haka yanzu muna sa ido kan kasuwar kuma shi ya sa muka dauki wannan matakin."

Najeriya ta fara amfani da tsarin amfani da kuɗaɗen ƙasashe da dama wajen auna kadarin kuɗinta don gujewa karya farashinta.

Asusun Lamuni na Duniya ya soki wannan tsarin kuma Babban Bankin Duniya ya dakatar da bayar da bashin dala biliyan 1.5 a wani mataki na son ingiza Najeriyar ta sauya manufofinta kan farashin Naira.

Ta wace hanya matakin karya farashin Naira zai shafi talaka a Najeriya?

Masanin tattalin arziki Dokta Muhammad Shamsuddeen na Jami'ar Bayero da ke Kano ya ce irin wannan matakin na lalata darajar kuɗi dama a kan talaka ya ke ƙarewa musamman tun da talaka ne yake zuwa kasuwa ya sai kayan masarufi.

Ya ce kuma da yawa kayan masarufi a Najeriya shigo da su a ke yi daga ƙasashen waje kuma wannan lalata darajar kuɗi zai shafi farashin kayan sannan ya ƙara tsawwala hauhawar farashi a ƙasar.

"Idan ba a manta ba a watan da ya gabata, hauhawar farashi a Najeriya ta kai kusan kashi 18.33 cikin ɗari wanda yanzu idan aka ci gaba da lalata darajar Naira, hauhawar farashin na iya kai wa kashi 20 cikin ɗari nan da watan gobe" a cewarsa.

Dokta Shamsuddeen ya ce wannan shi ne babbar wahala da talaka zai iya fuskanta.

Haka kuma, ya ce lalata darajar Naira na iya haifar da rashin aikin yi a ƙasar tun da kamfanoni da masana'antu da dama a Najeriya sun dogara ne da shigo da kaya daga kasashen waje domin sarrafawa - wannan na iya nufin injina ko kayan da ake sarrafawa don samar da wasu kayayyakin.

"Idan ya zama cewa waɗannan kayayyakin sun yi tsada sakamakon faɗuwar farashin Naira, babu shakka wasu masana'antun ba za su iya ci gaba da aiki ba dole su rufe masa'antun ko su rage kayan da suke yi," in ji Dokta Shamsu.

Ya ce wannan zai haifar da korar mutanen da suke aiki a waɗannan masana'antun.

"Talaka ne zai fi jin jiki"

Masanin ya ce ta ko wace fuska aka kalli wannan matakin an CBN, talaka zai wahala walau ta rashin aikin yi ko kuma ta hauhawar farashi.

Dokta Muhammad Shamsuddeen ya ce gwamnatin Najeriya na ƙoƙarin karya farshin ne saboda bashi da take so ta karɓa daga babban Bankin Duniya na dala biliyan 1.5 kuma bankin ya bai wa Najeriya Ƙa'idar haɗe farashin Naira na gwamnati da na kasuwa waje guda kafin ya ba da bashin.

Shi ya sa Najeriyar ke ta fafutukar ganin ta rage wa Naira daraja, farashin gwamnati ya dawo dai-dai da na kasuwa.

Sai dai Dokta Shamsuddeen ya ce yana ganin babu ma wata buƙatar rage darajar naira da babban bankin ya yi tun da har an zo matakin da naira 495-500 yake dai-dai da dala ɗaya a kasuwar bayan fage.

"Babu wata daraja da ta rage wa naira da har babban banki zai kare ta, kamata ya yi a saki kasuwa kawai ta yi wa naira ƙaidi. Yin hakan zai taimaka ta hanyoyi daban-daban," a cewarsa.

Ya ce hanya ta farko ita ce shi babban bankin ba zai riƙa bai wa wasu shafaffu da mai dala a farashin gwamnati ba kamar yadda ake zargi. Su kuma mutanen su sayar wa ƴan kasuwa a farashi mai tsada.

Ya ce wannan ne ke sawa kullum darajar naira tana ƙara faduwa.

"Abu na biyu shi ne Babban Banki CBN ya sauke wa kansa nauyin matsawa kansa sai ya sama wa naira daraja. Wannan na barazana ga ƴan kasuwa kuma yana hana masu zuba jari na ƙasashen waje shigowa Najeriya," in ji Dokta Shamsuddeen.

Ya ce abun da ya fi dacewa tun da an kai wannan matakin shi ne CBN ya cire hannunsa daga harkar sama wa naira daraja, ya bari kasuwa ta yi mata daraja kawai.

Kusan wannan ne karo na huɗu ko na biyar cikin shekara ɗaya da ta gabata da aka rage darajar naira a Najeriya.

Wannan ya haura kashi 30 cikin 100 na darajar nairar da aka rage cikin shekara guda - un tana naira 306 a watan Maris ɗin shekarar da ta gabata yanzu ta kai naira 410.