Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 28Article 451015

BBC Hausa of Friday, 28 May 2021

Source: BBC

'Yadda na tsira daga hatsarin jirgin ruwan da ya kifar da mutum 160 a Kebbi'

Har yanzu dai babu tabbaci kan abin da ya yi sanadin nutsewar jirgin Har yanzu dai babu tabbaci kan abin da ya yi sanadin nutsewar jirgin

Wata mata da ta tsira daga hatsarin da jirgin ruwa ya yi a cikin Kogi a jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya, ta ce ta ga tashin hankalin da ba za ta taɓa mantawa da shi ba na yadda ta ga halaka muraran.

Maryam Sani na daga cikin mutum 22 da hukumomi suka ce sun tsira a hatsarin daga cikin kusan 160 da ke cikin jirgin ruwan da ya kife a hanyarsa ta zuwa Kebbi daga Minna a ranar Laraba.

Har zuwa yanzu dai babu tabbaci kan abin da ya yi sanadin nutsewar jirgin.

Cikin fasinjojin har da mata da ƙananan yara da dama, kuma sun fito ne daga garin Lokon Mina mai yawan hada-hadar kasuwanci da ma'adinai a jihar Neja da ke yankin tsakiyar Najeriya.

Shugaban ƙaramar hukumar Ngaski ya ce ana ci gaba da aikin ceton, kuma zuwa yanzu gawa biyar aka gano, sannan mutum 10 cikin 22 da suka tsira na asibiti ana kula da shu.

Maryam wadda ta tsallake rijiya da bayan ta samu nasaarar tseratar da kanta har ma ta ceci wasu ƙarin mutum uku, biyu daga cikinsu yara da kuma wata matashiyar, bayan fashewar jirginsu.

Ta shaida wa BBC cewa: "Muna tsaka da tafiya kawai sai muka ji jirgi ya yi tsawa, sai muka ruɗe da salati. Ana haka sai jirgin ya rabe biyu.

"Sai na fara cewa mutanen ciki mu ciccire hijabanmu, masu riga su cire mu faɗa cikin ruwan, don idan muka tsaya a cikin jirgin to nutsewa za mu yi.

"Sai na jefa musu jarkoki muna kamawa. Da Allah Ya taimake ni sai yaran suka rirriƙe min jigida ni kuma na riƙe jarka ina iyo, ina ci gaba da jefa wa mutane jarka," a cewar Maryam.

Usama Danlami ma matashi ne ɗan shekara 20 da ya tsira a hatsarin, kuma a cikin mutanen da jirgin ya nutse da su akwai abokinsa Abdul wanda har yanzu ba a gano shi ba.

"Gaskiya na shiga damuwar ɓatan abokina don tare muke, kowa na tamabayata ina yake, inda na ce ban gan shi ba sai a shiga tashin hankali, ana fargabar ya mutu," in ji shi.

Iyaye da dangin da ba su ga ƴan uwansu da ƴaƴansu ba a yanzu suna cikin halin tashin hankali da fargaba. Cikinsu akwai mai ƴaƴa huɗu, wasu kuma ƴaƴa biyu.

A yanzu dai sun ce sun yanke ƙaunar samun ƴaƴan nasu da rayuka.

Wasu mazauna garin Wara sun shaida wa BBC cewa ba su taɓa ganin iftila'in jirgi mai muni kamar wannan ba, kuma sun yanke ƙaunar gano masu sauran rayuka a gaba.

Hukumar kiyaye kare afkuwar haɗurra ta jihar Kebbi ta ce mai yiwuwa ne gawarwakin su taso saman ruwa a yinin ranar Alhamis.

Buhari ya jajanta

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana hadarin jirgin ruwan na karamar hukumar Ngaski da ke jihar Kebbi a matsayin labari mai tayar da hankali.

Cikin sanarwar da mataimakinsa na musamman kan yada labarai Garba Shehu ya fitar, shugaban kasar ya mika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan mutanen da hadarin ya rutsa da su.

Wannan lamari na zuwa ne ƙasa da mako biyu bayan wani makamancinsa a jihar Neja mai maƙwabta da ya yi sanadin mutuwar mutum 40.