Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 04 09Article 450108

BBC Hausa of Friday, 9 April 2021

Source: BBC

Watakila Suarez ba zai buga wa Atletico tamaula zuwa mako uku

Luis Suarez, dan wasan Atletico Madrid Luis Suarez, dan wasan Atletico Madrid

Watakila Luis Suarez zai yi jinyar mako uku da hakan zai iya zama koma baya ga Atletico Madrid a shirin da take na lashe kofin La Liga na bana.

Suarez wanda ya ci kwallo 19 a La Liga a bana, ya yi rauni ne ranar Laraba a lokacin da yake atisaye a Atletico Madrid.

Kungiyar ce ta sanar da raunin da dan kwallon tawagar Uruguay ya yi, sai dai ba a fayyace lokacin da zai kammala jinyar ba, illa ana hasashen zai yi zaman mako uku kafin ya koma fagen taka leda.

Tun farko an dakatar da dan wasan mai shekara 34 daga buga karawa da Real Betis a gasar La Liga ranar Lahadi, sannan ba zai yi fafatawa da Eibar da Huesca da kuma Athletic Bilbao ba.

Wannan raunin da Suarez ya yi zai bai wa Moussa Dembele damar buga wasa, wanda ya koma kungiyar daga Lyon a watan Janairun 2020, amma minti 42 kacal ya yi wa Atletico Madrid.

Atletico ta bayar da tazarar maki 10 a teburin La Liga a watan Janairu, sai dai ranar Litinin tazarar ta koma maki daya tal, bayan da Barcelona ta doke Valladolid.

A kuma karshen makon Atletico ta yi rashin nasara a hannun Sevilla da ci 1-0 a gasar ta kasar Spaniya.

Haka kuma Atletico Madrid za ta buga wasa da Betis ba tare da Marcos Llorente wanda shi ne na biyu a ci wa mata kwallaye, bayan Luis Suarez a kakar nan.