Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 03 21Article 449786

BBC Hausa of Sunday, 21 March 2021

Source: BBC

Wasu 'yan Najeriya na adawa da kashe Biliyan 400 don gyaran matatar mai ta Fatakwal

Hoton matatar man fetur mafi daɗewa a ƙasar ta Fatakwal, dake jihar Rivers Hoton matatar man fetur mafi daɗewa a ƙasar ta Fatakwal, dake jihar Rivers

Wasu 'yan Najeriya sun fara bayyana adawarsu ga shirin gwamnatin ƙasar na kashe zunzurutun kuɗi har Dala Biliyan guda, domin gyara matatar man fetur mafi daɗewa a ƙasar ta Fatakwal, dake jihar Rivers.

Majalisar zartarwa ta ƙasa ce ta amince da fitar da waɗannan kuɗaɗe don yin gagarumin aikin a ranar Laraba.

Ita dai wannan matata ta shafe fiye da shekaru 50 tana aiki, kafin fara samun matsala a shekarun baya bayan nan, lamarin da ake ganin ya haifar da gagarumin cikar wajen tace man a cikin gida.

To sai dai yayin da gwamnatin ke cewa akwai buƙatar gyara matatar domin bunƙasa tace mai, wasu 'yan Najeriya na da ra'ayin cewa almubazzaranci ware kuɗi masu yawa irin wadannan don gyara matatar mai guda, kuma tsohuwa.

''Duk mai hankali ya san cewa duk abin da aka ce tsohon abu ne to gyaransa sai a hankali, na biyu matatar man nan wani kamfanin Japan ne ya yi, amma yanzu an ce 'yan Italiya ne za su yi wannan gyaran, anya za su iya kuwa ?, na uku an ce za a shafe fiye da watanni 44 ana gyaran, wannan ma wani abu ne dake tayar mana da hankali'' inji Abubakar Idris, wani ɗan Najeriya da ya bayyanawa BBC ra'ayinsa.

Ya kuma ƙara da nuna damuwa a kan makudan kuɗaɗen da aka ware don yin aikin, wanda a ganinsa da za a yi amfani da su wajen samar da wasu matatun man za a iya samar da ƙanana da yawa.

    'Yawan gyara matatun man Najeriya zai ba da kafar cin hanci' Babu gaskiya a jita-jitar sake ƙara farashin man fetur a Najeriya – NNPC Me ake nufi da kasuwa ta yi halinta wajen sayar da fetur?
Ita kuwa Janet, cewa ta yi da kashe wadannan kuɗaɗe gwara ma a ce wata sabuwar matatar man za'a yi.

''A tunanina wannan gyara kashe kudi ne, ba lallai bane ma ya yiwu, sannan samun kayan da za a yi amfani da su ma wata wahalarce ta daban, don haka a sake tunani'' inji ta.

Shi kuwa Isiyaku daga jihar Zamfara a Najeriyar damuwa ya nuna a kan yadda aka sha fitar da kuɗi irin wadannan don yin wani aiki a baya, amma sai a rasa inda aka yi da su sama ko ƙasa.

''Ya kamata a ji tsoron Allah, a kamanta gaskiya, idan ma an cire kuɗin a cire makimanta ba irin waɗannan ba, kuma ai ance kuɗin za su iya gina wata matatar man, toh ina amfanin cire kudin da za a iya yin sabon abu don gyara tsoho ?'' a ra'ayin Malam Isiyaku.

An dai shafe fiye da shekaru 20 ana ƙoƙarin gyara wannan matatar man fetur, amma hakan bai yiwu ba, dalilin kenan da wasu ke ganin cewa ba lallai ne a wannan karon ma ya kasance an yi gyaran ba.