Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 03 23Article 449826

BBC Hausa of Tuesday, 23 March 2021

Source: BBC

Wasu jiga-jigan kabilar Yarabawa sun nesanta kansu daga ballewa daga Najeriya

Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu

Wasu jiga-jigan Yarabawa sun nesanta kansu daga matakin da mai ikirarin fafutukar nema wa kabilarsu 'yanci ya dauka na cire Yarabawa daga Najeriya domin kafa kasarsu.

A kwanakin baya ne Sunday Igboho ya ce kabilar Yarabawa za ta balle daga Najeriya saboda rashin adalcin da ake yi mata.

A cewarsa, shi da wasu masu ra'ayi irin nasa sun dauki matakin ballewa daga Najeriya ne sakamakon kashe-kashen da makiyaya suke yi wa Yarabawa a jihohin kudu maso yammacin kasar.

Ya yi kira ga dukkan Yarabawa su amince da matakan da shugaban kungiyar kafa kasar Yarabawa ta Nigerian Indigenous National Alliance for Self-determination, Farfesa Banji Akintoye yake dauka na tabbatar da kasar Yarabawa mai cin gashin kanta.

A baya bayan nan Sunday Igboho ya jagoranci wasu masu ikirarin kare hakkin Yarabawa inda suka rika korar Fulani makiyaya daga jihohin kudu maso yammacin Najeriya.

Ya zargi Fulanin da ke yankin da kitsa garkuwa da mutane da kashe-kashe da kuma wasu laifuka da ke faruwa a yankin.

Hakan ya janyo kakkausan martani daga hukumomin kasar da kuma mazauna arewacin kasar.

Hasalima a watan Janairun da ya wuce, mai magana da yawun shugaban Najeriya, Malam Garba Shehu, ya shaida wa BBC cewa Babban Sifeton Ƴan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya bayar da umarni a kamo Sunday Igboho.

A cewarsa, babban jami'in 'yan sandan ya ba da umarnin ne ga kwamishinar ƴan sandan jihar Oyo, Mrs Ngozi Onadeko, inda ya bukaci ta kai masa shi Abuja.

Amma har yanzu ba a kama shi ba kuma ana ganinsa yana yawo a bainar jama'a.

'Ba da mu ba'

Sai dai wasu jiga-jigan kabilar Yarabawa sun nesanta kansu da ikirarin da Mr Igboho ya yi na kafa kasar Yarabawa masu 'yanci.

Gwamnan jihar Ondo da ke kudu maso yammacin Najeriya, Rotimi Akeredolu, ya bayyana cewa jiharsa ba ta cikin wadanda ke son ballewa daga Najeriya domin kafa kasar Yarabawa.

Gwamnan ya yi wannan bayani ne a wurin bikin rantsar da sabuwar Sakatariyar Gwamnatin jihar Ondo Princess Oladunni Odu, da wasu mashawarta na musamman ga gwamnatinsa a ranar Litinin.

Shi ma Sarkin al'umar Yarabawa na Ibadan Saliu Adetunji ta bakin mataimakinsa kuma daraktan yada labarai, ya nesanta masarautarsa da wannan batu.

Ya shaida wa BBC cewa ikirarin da Sunday Igboho yake yi sirme ne kawai.

"Idan za a dauki mataki irin wannan ana bukatar tattaunawa akai, ba wai mataki ne da za dauka a Ibadan kuma lokaci daya ka ce a yi haka ba. Wannan ba zai yiwu ba.

Al'ummar Yarabawa fa ba yadda mutane suke kallon ta take ba. Yana da muhimmanci a tuntubi masu ruwa da tsaki kafin daukar irin wannan matakin," in ji basaraken.