Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 05 02Article 450546

BBC Hausa of Sunday, 2 May 2021

Source: BBC

Waiwaye: Tsayar da ranar zaɓen 2023 da martanin Buhari ga Ortom

Shugaba Muhammadu Buhari Shugaba Muhammadu Buhari

Ga wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a makon da ya gabata a Najeriya, daga Lahadi 25 ga Afirilu zuwa Asabar 1 ga Mayu.

Yadda mutane suka rika tserewa daga Geidam don neman mafaka

A Najeriya mutanen Geidam sun ci gaba da tserewa daga garin sakamakon kutsen da 'yan Boko Haram suka yi tun ranar Juma'a.

Shaidu sun ce sun tsere ne saboda gudun kada a ritsa da su a musayar wutar da ake yi tsakanin sojojin Najeriya da mayaƙan Boko Haram.

Haka zalika, an fafata tsakanin 'yan Boko Haram da sojoji a garin Mainok na jihar Borno mai maƙwabtaka, har wasu rahotanni na cewa harin ya ritsa da wasu sojoji.

A baya-bayan nan dai ƙungiyar Boko Haram na zafa-zafa hare-hare a sassa daban-daban na arewa maso gabashin Najeriya.

Kashe DPO da 'yan sanda 8 a Jihar Kebbi

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta tabbatar da mutuwar wani DPO da jami'ansa takwas a Jihar Kebbi da ke arewacin kasar.

Kakakin yan sandan na Jihar Kebbi ASP Nafi'u Abubakar ne ya tabbatarwa BBC da faruwar lamarin, wanda ya faru a ranar Lahadi.

"Da misalin karfe 2:30 na rana ne DPO na Kasaba ya samu labarin an kai hari wani kauye da ake kira Makuku da wasu kauyuka da ke kewaye da shi, nan da nan ya debi yaransa su takwas da nufin kai dauki bayan fafatawa kuma anan suka gamu da ajalinsu," in ji ASP Nafi'u.

Sukar da Matar Bola Tinubu ta yi wa Sanatan da ya ce babu tsaro a Najeriya

Wasu 'yan majalisar dattawan Najeriya sun yi musayar zafafan kalamai sakamakon rashin tsaron da ke ci gaba da ta'azzara a kasar.

Sanatocin, Smart Adeyemi daga jihar Kogi da Remi Tinubu daga jihar Lagos, suna cikin wadanda suka bayar da gudunmawa yayin muhawarar da majalisar dattawan kasar ta gudanar ranar Talata.

Majalisar ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya zage damtse domin magance rashin tsaron da kasar ke ci gaba da fama da ita tana mai shan alwashin ganawa da shi a kan batun.

A nata bangaren, majalisar wakilan kasar ta bukaci Shugaba Buhari ya ayyana dokar ta-baci a kan matsalar tsaro.

'Yan majalisun na yin kiran ne a yayin da ake ci gaba da kai hare-hare a kusan dukkan sassan kasar - daga rikicin masu garkuwa da mutane da 'yan fashin daji, zuwa hare-haren 'yan Boko Haram da na masu son ballewa daga kasar na kungiyar IPOB.

Tsayar da ranar zaben 2023 da INEC ta yi

Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta tsayar da ranar zaɓen 2023 a ƙasar.

Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin taron yini ɗaya na sauraren dokar laifukan Zabe ta 2021, wanda kwamitin Majalisar Dattawa kan INEC ya shirya.

"Bisa dokar da aka kafa hukumar, zaɓen 2023 zai kasance ranar Asabar 18 ga watan Fabrairun 2023, wanda ya rage saura shekara ɗaya da wata Tara da mako biyu da kwana shida daga yau."

Shugaban Hukumar ya ce suna fatan tsara jadawalin zaɓen da zarar an kammala zaɓen gwamnan jihar Anambra wanda za a gudanar a ranar 6 ga Nuwamban 2021.

Kalaman Obasanjo kan matsalar tsaro

Tsohon Shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya ce yana da yakinin cewa matsalolin tsaron da ake fama da su a sassan kasar ba za su ga bayan Najeriya ba har ta kai ta durkushe yana mai cewa kasar za ta fita daga kangin da ta tsinci kanta a ciki.

Ya bayyana haka ne a wani taro da aka yi domin karrama shugaban kungiyar kiristoci ta Najeriya, CAN wato Dakta Samson Ayokunle.

A jawabinsa, Obasanjo ya ce yana da imanin cewa Najeriya ba za ta durkushe ba duk da karuwar tabarbarewar tsaro.

Ba Obasanjo ne kadai yake da irin wannan fahimta ba, wasu gwamnoni da suka halarci taron irinsu Dapo Abiodun na Ogun da Seyi Makinde na Oyo na ganin za a samu mafita.

Tsage gaskiyar Ganduje kan cin hanci a Najeriya

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce Najeriya ba za ta taba ci gaba ba saboda cin hanci da rashawar da ya dabaibayeta.

Ganduje ya ce babu yadda za a yi kasar nan ta ci gaba da irin wannan cin hanci da rashawar da ake fama da shi a Najeriya.

"Za ku yarda da ci idan na ce cin hanci yana kashe mu. Maganar gaskiya ita ce ba inda kasar za ta je da wannan cin hanci. Ba za mu motsa ko ina ba," in ji Ganduje.

Ganduje ya bayyana hakan ne ya yin kaddamar da wani kwamitin na mutum takwas kan wasu dabarun yaki da rashawa a jihar.

Halin da ake ciki game da wutar lantarki a Mambila

Ministan makamashi a Najeriya, Injiniya Sale Mamman ya sanar da cewa ana ci gaba da shirye-shiryen aikin wutar lantarki na Mambilla.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, minista ya bayyana cewa ya gana da jami'an kamfanin China Gezhouba Group International, wanda zai ja ragamar aikin.

Ya ce gwamnatin Najeriya da duka masu ruwa da tsaki a shirye suke su tabbatar an kammala aikin.

Sai dai ya ce ƙalubale ɗaya da ma'aikatarsa ke fuskanta ita ce rikicin shari'a tsakaninta da kamfanin da aka fara bai wa kwangilar aikin, Sunrise Group, inda ya ce wannan ya ƙara mayar da aikin baya.

Injiniya Sale Mamman ya ce a halin yanzu, ana kan gaɓar kammala sa hannu a ƙa'idojin kwangilar kuma ya ce nan ba da jimawa ba za a fara aikin na Mambilla.

Sa-in-sar Buhari da Gwamna Samuel Ortom

Shugaban Najeirya Muhammadu Buhari ya ce abin takaici ne irin yadda gwamnan jihar Benue Samuel Ortom yake zarginsa da aikata wasu laifuka.

Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a wata sanarwa da mai magana da ywunsa Malam Garba Shehu ya aike wa manema labarai ranar Juma'a da safe.

Ya mika jajensa ga al'ummar jihar ta Benue wadanda suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren da aka kai musu a baya bayan nan.

Rahotanni sun ambato Gwamna Ortom yana zargin Shugaba Buhari da mara wa makiyaya baya a kashe-kashen da yake cea sun yi a jihar ta Benue.

Sai dai shugaban kasa ya kara da cewa babu kamshin gaskiya a zarge-zargen yana mai cewa "babu wata gwamnatin da take da hankali da za ta ji dadin irin wadannan kashe-kashe na sojoji da mutanen da ba su ji ba ba su gani ba da ke zaune a sansanonn 'yan gudun hijira."

Bukatar Rabaran Ejike Mbaka ta a stige Buhari

A dai cikin makon ne, fitaccen malamin Cocin Katolikan nan da ke Najeriya, Rabaran Fada Ejike Mbaka, ya ce ya kamata shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sauka daga mulki idan ba haka ba a tsige shi.

Rabaran Fada Mbaka, wanda a baya a goyi bayan shugaban kasar, ya kara da cewa ya yi kiran ne saboda Shugaba Buhari ya gaza shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi Najeriya.

Malamin Cocin ya bayyana haka ne a gaban dimbin mabiyansa a Enugu da ke Kudu Maso Gabashin Najeriya.

"Idan da a kasashen da aka ci gaba ne da tuni Shugaba Buhari ya ajiye mukaminsa. Ku ambato ni a koina cewa na yi kira ga shugaba Buhari ya sauka daga mulki tun da girma da arziki.

Muna kuka ne saboda ba mu da jagora...idan ba za ka iya mulki ba, ka sauka ko a sauya ka...ko dai Buhari ya sauka da kansa ko kuma a tsige shi.."

Rahoton Jihar Kaduna kan matsalar tsaro

Wani rahoto da ma'aikatar tsaro da harkokin cikin gida ta jihar Kaduna ta fitar ya nuna cewa daga 1 ga watan Janairu zuwa 31 ga watan Maris na 2021 an kashe mutum 323 tare da yin garkuwa da mutum 949 a jihar.

Samuel Aruwan, Kwamishinan da ke kula da ma'aikatar ya bayyana cewa alƙaluman na nuna mutanen da suka rasa rayukansu sanadiyyar ayyukan ƴan bindiga da fashin daji da garkuwa da mutane da hare-haren ramuwa, ciki har da mahara da ƴan bindigar da jami'an tsaro suka kashe.

Sai dai ya ce bai haɗa da jami'an tsaro da suka mutu a bakin aiki ba.

Haka kuma, alƙaluman ba su haɗa da mutanen da suka rasu sanadiyyar haɗurran abubuwan hawa da kisan kai ba.