Vous-êtes ici: AccueilAfriqueBBC2021 03 15Article 449658

BBC Hausa of Monday, 15 March 2021

Source: BBC

Waiwaye: An sace 'mata 50' a Katsina cikin kwana biyu, Buhari ya bai wa 'yan fashi wa'adi

Shugaba Muhammadu Buhari Shugaba Muhammadu Buhari

Kamar yadda aka saba, wannan makon ma mun duba muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya, ciki har da kuɗin makamai da Babaguno ya ce ba gansu ba da fafatawa tsakanin sojoji da Boko Haram.

Ba mu san inda kudin makamai suka maƙale ba - Babagana Monguno



Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno ya ce har yanzu ba a san yadda aka yi da makudan kudaden da shugaba Buhari ya bayar don sayen makamai da sauran kayan aiki don yaki da matsallolin tsaro da suka addabi kasar ba.

A hirarsa da BBC Monguno ya bayyana cewa gwamnati na bakin kokarinta wajen shawo kan matsalar tsaron da ake ci gaba da fuskanta, da wasu 'yan Najeiya ke ganin gwamnati ba da gaske ta ke yi ba domin tana ta jan kafa game da al'amarin.

"Babu wanda ya san abin da aka yi da wadannan kudaden, amma da yardar Allah shugaban kasa zai bincika domin a gano inda aka kai su ko kuma inda kayan suka shiga," in ji Monguno.

Kungiyar gwamnoni ma in ji jami'in tsaron sun fara magana a kan cewa "an bayar da kudade ta ko ina amma babu abin da aka yi da su, saboda haka na tabbatar shugaban kasa tun da ba mai wasa da hakkin al'umma bane, zai taimaka."

Sai dai ofishin Munguno ya fitar da sanarwa yana mai musanta cewa mai bai wa shugaban shawara bai ce kuɗin makamai sun ɓata a hannun tsoffin shugabannin tsaro ba.

'Yan bindiga sun sace ɗalibai mata 39 a Jihar Kaduna



Gwamnatin Jihar Kaduna ta tabbatar da sace ɗalibai 30 daga Kwalejin Horar da Harkokin Noma da Abubuwan da suka shafi Gandun Daji ta gwamnatin tarayyya wato Federal College of Forestry Mechanisation a unguwar Mando a cikin garin Kaduna.

Daga baya gwamnatin ta ce mutum 39 ne ba a gani ba ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

Kwamishinan harkokin tsaro na jihar, Samuel Aruwan a cikin wata sanarwa ya ce kawo yanzu ba'a san inda dalibai 30 suke ba amma Sojojin Najeriya sun ceto mutane 180 da akasari daliban kwalejin.

"Sojojin Najeriyar sun samu nasarar ceto mutanen 180; dalibai mata 42, da malamai takwas da kuma dalibai maza 130. Amma kuma har yanzu ba a gano sauran dalibai maza da mata kusan 30 ba", in ji Aruwan.

'Yan bindigar su da yawa sun kai hari a makarantar ne da misalin karfe sha daya da rabi na daren Alhamis, inda suka sace dalibai da dama har da malamai.

Labarin ƙara kuɗin man fetur ƙarya ne - Ministan man fetur



Ƙaramin ministan man fetur na Najeriya ya nemi afuwar 'yan ƙasar kan "wahalhalun da suka shiga" bayan ɓullar labarin ƙarin kuɗin man a safiyar yau Juma'a, wanda ya bayyana da "abin baƙin ciki".

Da sanyin safiyar Juma'a ne hukumar kula da farashin fetur (PPRA) ta mayar da litar man zuwa naira 212 daga 163, amma daga baya ta ce yadda ake cinikin man a kasuwa kawai ta bayyana ba ƙari a kan yadda talakawa ke saya ba.

Timipre Sylva ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa, yana mai cewa daga shi har Shugaba Muhammadu Buhari, wanda shi ne babban ministan man fetur, babu wanda ya amince da ƙarin zuwa naira 212 kan kowace lita.

Ya ƙara da cewa duk da bai san daga inda aka samu labarin ba, "ina so na tabbatar muku cewa ƙarya ce zallanta".

Lamarin ya jawo ɓacin rai daga 'yan Najeriya, inda suka riƙa sukar gwamnatin Shugaba Buhari, wadda ta haƙiƙance cewa ba za ta ƙara kuɗin man ba a cikin watan Maris.

PPRA ta goge bayanan farko da ta wallafa a shafinta na intanet game da ƙarin kuɗin man.

Buhari ya bai wa ƴan bindigar Zamfara wa'adin wata biyu su miƙa wuya



Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya bai wa ƴan bindigar da ke jihar Zamfara a arewacin Najeriya wa'adin wata biyu su miƙa wuya.

Gwamnan Zamfara Bello Matawalle ne ya faɗi hakan a wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin a ranar Talata da dare.

Gwamna Matawalle ya kuma ce shugaban ƙasar ya bayar da umarnin kai ƙarin dakarun tsaro 6,000 jihar don murƙushe ƴan bindigar idan har suka ƙi miƙa wuya.

Jawabin gwamnan na zuwa ne a daidai lokacin da hare-haren ƴan fashi a ƙauyuka da kuma satar mutane ke ƙaruwa a jihar.

Gwamna Matwalle ya ce Shugaba Buhari ya yi wannan alƙawari ne a lokacin da ya kai wata ziyarar aiki Abuja don gana wa da shugaban da sauran manyan masu ruwa da tsaki kan sha'anin tsaro, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ambato.

An yi gumurzu tsakanin sojoji da mayaƙan Boko Haram a hanyar Damaturu-Maiduguri



An yi arangama tsakanin sojojin Najeriya da mayaƙan Boko Haram a kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri inda shaidu suka ce sun ga mutum biyu na ci da wuta a gefen titi.

Bayanai na cewa lamarin ya auku ne da safiyar Lahadi, 8 ga watan Maris, a tsakanin garuruwan Jakana da Mainok da Beneshiekh, inda ƴan Boko Haram suka yi yunƙurin kutsawa wani sansanin soji, sai dai sojojin da taimakon yan uwansu na sama sun yi nasarar daƙile aniyar tasu.

Wasu rahotanni sun ce an kashe ƴan Boko Haram da dama a yayin musayar, kana an lalata motoci da makamai, amma babu bayanin ko an kashe wasu daga cikin sojojin.

Lamarin ya haifar da tsayawar ababen hawa da ke tahowa daga Damaturu, da zummar shiga Maiduguri.

Wani direba da ya isa wajen da fasinjojinsa jim kadan bayan faruwar lamarin ya shaida wa BBC cewa da idonsa, ya ga mutum biyu na ci da wuta lokacin da suka isa wajen.

An sace 'mata 50' a Katsina cikin kwana biyu



Rahotanni daga jihar Katsina a arewacin Najeriya na cewa 'yan bindiga sun yi awon gaba da wasu mata kimanin 30 daga wani kauye a kudancin jihar da tsakar daren Litinin.

Hakan ya zo ne bayan da wasu bayanan kuma suka ce maharan sun sace wasu matan fiye da 20 daga wasu kauyukkan biyu a ranar Lahadi.

Sai dai jami'an tsaro a jihar ba su tabbatar da faruwar lamuran ba kawo yanzu.

Ya zuwa yanzu babu tabbacin ko 'yan bindigar sun sako mutanen.

Gwamnatin Neja za ta ba ƴan banga bindigogi don yaƙi da masu garkuwa da mutane



Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello ya yi alƙawarin bai wa kungiyar yan sa kai bindigogi don yaki da yan bindiga da suka addabi jihar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnan ya gana mayaƙan sa kan sama da 200 a unguwar Kasuwan Garba, inda ya tabbatar masu da cewa zai ba su bindiga don su iya tunkarar "maƙiyan" jihar.

Ya kai ziyara yankin ne don karfafa wa ƴan sa kan gwiwa.

Hare-haren ƴan bindiga da kashe-kashe da satar mutane don kuɗin fansa sun zama ruwan dare a jihar, inda a baya-bayan nan ma aka yi garkuwa da wasu ɗalibai a makarantar sakandire ta Kagara.

Wasu ƴan bindiga a jihohin Neja da maƙwabtanta a yankin arewa maso yammacin sun buƙaci mayakan sa-kai su ajiye makamai idan ana so su mika wuya su daina kai hare-hare.

Zulum ya gano ɗaruruwan ƴan gudun hijira na bogi masu wawushe abinci



Gwamnan Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya yi wa wani sansanin ƴan gudun hijira shigar ba-zata inda ya gano ɗaruruwan ƴan gudun hijirar na bogi.

Sanarwar da gwamnatin Borno ta aike wa BBC ta ce daga cikin ƴan gudun hijira 1,000 da ke cikin kundin jami'an agaji, 650 daga cikinsu na bogi ne.

Sanarwar ta ce gwamnan ya kai ziyara ne a sansanin kwalejin Mohammed Goni MOGOCOLIS inda ake kula da mutanen ƙaramar hukumar Abadam a arewacin Borno da rikici ya raba da gidajensu.

"Gwamna Zulum ya yi shigar ba-zata ne sansanin ƴan gudun hijirar da tsakiyar dare tare da rufe sansanin domin tantance yawan ƴan gudun hijirar," in ji sanarwar.

Sannan ta ce gwamnan ya yi hakan ne domin gano masu ƙaryar cewa ƴn gudun hijira ne da ke shafe kwanaki a sansanin suna karɓar abincin da aka tanadar wa ƴan gudun hijira, kuma idan dare ya yi su tafi gidajensu.

Kamaru ta mayar da ƴan gudun hijirar Najeriya 5,000 gida



Hukumomin Kamaru karkashin jagorancin Minista Paul Atanga Nji, sun mayar da ƴan gudun hijirar Najeriya 5,000 gida, inda suka miƙa su ga gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum.

An miƙa mutanen ne ranar Litinin a unguwar Amchide da ke kan iyakar kasashen biyu.

Ƴan gudun hijirar na cikin dubban ƴan Najeriya da suka tsere daga Borno a shekarar 2014 zuwa sansanin ƴa gudun hijira na Minawao a Mokolo da ke yankin arewacin Kamaru don gujewa tashin hankalin Boko Haram.

Minista Paul Atanga Nji ya snaar da cewa Shugaba Paul Biya ya amince a bai wa ƴan gudun hijirar 5,000 tallafin kayan abinci da katifu da barguna.

Haka kuma, ministan ya yaba wa Gwamna Zulum kan gidajen da ya gina wa ƴan gudun hijirar inda za su fara sabuwar rayuwa.

Shi ma Gwamna Zulum ya raba wa mutanen kayan abinci da sauran kayan amfani.

Ya bai wa ko wane namiji mai iyali Naira 30,000 sannan aka ba ko wace mace Naira 10,000 da atamfa.

Farashin man fetur ya kai dala 71 karon farko bayan cutar korona



A karon farko bayan ɓarkewar annobar cutar korona, farashin ɗanyen man fetur samfurin Brent ya kai dala 71.28 kan kowace ganga a kasuwar duniya.

Ƙaruwar farashin ya biyo bayan matakin da ƙungiyar ƙasashe masu arzikin mai ta Organisation of Petroleum Exporting Countries, OPEC (OPEC) da ma waɗanda ba mambobin ƙungiyar ba, inda suka amince su ƙara yawan adadin man da suke fitarwa kasuwar.

Kafin taron ministoci mambobin ƙungiyar na ranar Alhamis, 4 ga Maris, farashin man yana kan dala 65 ne.

Yayin da samfurin Brent ya kai dala 71, samfurin Bonny Light wanda Najeriya ke haƙowa yana kan dala 67.69 ya zuwa ranar Talata.

Hakan na nufin an samu ƙarin dala 30 kenan kan farashin da gwamnatin Najeriya ta saka a kasafin kuɗinta na 2021, inda yake kan dala 40 a kowace gangar mai da kuma haƙo ganga miliyan 1.8 a kowace rana.